EFCC Ta Maka Tsohon Ministan Jonathan, Kabiru Turaki A Kotu

108

A ranar Litinin ne Hukumar Hukunta Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC ta maka tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Turaki a kotu, kamar yadda rahoton jaridar Intanet ta PREMIUM TIMES ya bayyana.

Tsohon Ministan dai bai amsa laifukan da hukumar ta EFCC ke zargin sa da aikatawa ba.

EFCC ta maka Mista Turaki, hadiminsa da wasu kamfanoni biyu a kotu bisa tuhume-tuhume 16 na zargin kashe kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba.

Sauran waɗanda ake ƙarar su ne Sampson Okpetu, wanda ya yi aiki a matsayin Mataimaki na Musamman Ga Mista Turaki, sai kamfanin Samtee Essentials Limited da Pasco Investment Limited, waɗanda ake zargin mallakin Mista Okpetu ne.

An gurfanar da su ne ranar Litinin a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo ta Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.

Mista Turaki, wanda Babban Lauya ne na Najeriya, SAN ya jagoranci Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Al’amuran Gwamnatoci tsakanin 2013 zuwa 2015, ya kuma zama Minista Mai Sa Ido na Ƙwadago daga 2014 zuwa 2015 a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan.

Shi ma wanda ake ƙara na biyu, Mista Okpetu, ya musanta laifukan da ake zargin sa da aikatawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan