COVID-19: Abin Takaici Ne Yadda Aka Daina Sallolin jam’i- Ganduje

3

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nuna damuwa bisa yadda aka daina sallolin jam’i sakamakon cutar coronavirus, a cewar rahoton jaridar Intanet ta Kano Focus.

Majiyarmu ta ce Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne ranar Talata lokacin wani taron tattaunawa da sarakunan Kano da jami’an lafiya kan yadda za a yaƙi cutar.

“Abu ne mai raɗaɗi yadda ba ma iya gudanar da sallolinmu na jam’i a masallaci. Amma ba abinda za mu iya yi a kan haka.

“Yin musafaha a yayin gaisawa ba abu ne mai yiwuwa ba yanzu. Amma ba abinda za mu iya yi a yanzu.

“Mu yi aiki tare don karya yaɗuwar cutar”, in ji Gwamna Ganduje.

A jawabinsa, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, wanda ya yi jawabi a madadin sauran sarakunan, ya tabbatar wa da gwamnatin jihar Kano goyon bayansu wajen yaƙar cutar COVID-19.

Sarki Bayero ya ce kodayaushe gwamnatin jihar Kano tana shigar da sarakunan gargajiya wajen yaƙi da cutar.

Taron ya samu halartar mambobin kwamitocin yaƙi da COVID-19 na ƙasa da na jiha, da kuma sarakunan Kano, Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan