A Lokacin Ina Saurayi Ƴan Mata Ba Sa Kulani Saboda Gajarta – El-Rufai

54

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, ya wallafa bidiyon wata hira da ya taɓa yi a shafinsa na tiwita da ɗan wasan barkwancin nan Teju Babyface.

Bidiyon wanda aka dauka a shekarar 2010, inda gwamnan yayi hira da dan wasan barkwancin, El-Rufai ya ce shi ne sakatare janar na gajerun mutane na Najeriya. Ya kuma bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta akan rashin tsawon da yake da shi.

“A da ni ne sakatare janar… a lokacin da na ke tsakanin shekaru 20 na fuskanci ƙalubale sosai saboda gajarta ta, saboda kun san lokacin duka kyawawan ƴammata sun fini tsawo.

“Amma a hankali komai ya zo ya wuce, har na samu kyakkyawar mata mai ilimi na aura, wacce na fita tsawo da kaɗan.

Na tuna wannan hirar da nayi da Teju Babyface a shekarar 2010…lokaci yana tafiya sosai. Yanzu mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shi ne shugaban kungiyar gajerun mutane ta Najeriya.”

Turawa Abokai

5 Sako

  1. Tunda har za’abari ayi kasuwa to sallar jam’i da na juma’a shima yakamata abari ayi. cuta bazata kamaka a kasuwaba se a masallaci?

  2. YA kamata kowa dake Nigeria Ya gane covid19 karya ce tunda har yanzu ba.a taba nuna mana ya take bah ita cutar mun ga dai ta yan China amma yata yan Nigeria take al rufai gareka inace ta kama kah kuma har kana iya futowa media kai xance va.ance kilace mutum ake bah

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan