Manyan Ayyukan Alherin Da Pantami Ya Yi Waɗanda ‘Yan Najeriya Za Su Daɗe Suna Mora

151
  • Sheikh Dr. Isa Ali Pantami malamin addinin musulunci ne da yayi kaurin suna wajen fadar gaskiya da kuma tunatar da masu mulkin irin nauyin da ya rataya akansu.
  • Yana da ilimin addini da na boko, yana kuma sha’awar bayar da gudunmuwarsa a fagen al’amuran yau da kullum.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara gabatar da shi cikin harkokin siyasar kasar nan a zangon mulkinsa na farko a matsayin shugaban hukumar NITDA, bayan ganin aikinsa yayi kyau ne ya damka masa ragamar jagorancin hukumar sadarwa ta kasa baki daya.

Mutane da yawan gaske sun kyautata masa zato lokacin da sunansa ya fito cikin kunshin wadanda shugaba Buharin zai nada a ministoci duba da gogewarsa, karancin shekarunsa da kuma irin hubbasar da yayi na ingantawa da aiwatar da manyan aiyuka a hukmar NITDA.

Sheikh Dr. Isa Ali Pantami

Da zamansa minista zuwa wannan lokacin yayi wasu manyan aiyuka jiga-jigai da yan Nijeriya zasu dade suna mora kuma zasu inganta rayuwar mutane da yawan gaske. Wasu daga ciki sun hadar da;

  • Sanya ido kan kamfanunuwar sadarwa
Sheikh Dr. Isa Ali Pantami

Kafin zuwan Pantami, abu ne sananne kan yadda wadannan kamfanoni suka mayar da yan Nijeriya saniyar tatsa ko kuma suke matsarsu kamar tukunza ta hanyar cire musu kudade babu gaira babu saba tare da sanya su cikin tsarin da za’a ke cirar musu kudi ba tare da sani ko amincewarsu ba. Wanna duk ya zama tarihi ga yan Nijeriya yanzu.

Haka zalika cutar da ake yiwa masu amfani da intanet (Data Bundle) shi ma yanzu ya ragu sosai kuma farashin ya sakko kasa.

  • Sauyawa hukumar sadarwa ta kasa akalar yadda take tafiyar da aiyukanta
Sheikh Dr. Isa Ali Pantam da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Baro-baro daga waje kowa na iya yarda cewa sunan hukumar sadarwa ta kasa (Ministry of Communiation) ya sauya zuwa hukumar sadarwa da tattalin arzikin zamani (Ministry of Communication and Digital Economy) wannan ya faru bayan zamowar Dr. Isa Pantami Minista.

Amma sauye sauyen ba’a iya sunan kadai ya tsaya ba kusan kamar ka ce ciki da waje sauyin ya shafa. Jan kafar da ake yi wajen yanke hukunci a sassan hukumar shi ma ya ragu matuka tunda har a Twitter Ministan na bayar da umarnin a bincika matsala ayi maganinta musamman korafi.

  • Kaddamar da zaman majalisar zartarwa ta kasa ta intanet a karon farko a Nijeriya
Taron majalisar zartarwa ta kasa

An sha fasa taron majalisar zartarwa ta kasa bisa wasu dalilai, watakil rashin lafiya ko tafiyar shugaban kasa da mataimakinsa da sauransu; amma cikin jajircewarsa Dr. Ali Pantami, yanzu da ake fama da annobar Korona ake da bukatar nisantar juna da yin aiki daga gida, hukumar da yake shugabanta ta kirkiro hanyar gudanar da tattaunawar kowa na gida ko ofishinsa (virtual meeting) a karon farko a tarihin Najeriya.

Wadannan na daga cikin aiyukan da ministan yayi wanda yan Nijeriya zasu more su tsawon lakaci.

Sheikh Dr. Isa Ali Pantami
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan