Yadda Cutar Makanta Ta Zamemin Alheri A Rayuwata – Yahaya Makaho

172

Yahaya Usman wanda duniya ta fi sani da Yahaya Makaho ya bayyana cewa ya tsallake bara, inda ya kama sana’ar waka domin kula da kansa da kuma iyalinsa.

Mawakin ya gamu da makanta yana dan shekara uku sanadiyyar wata cuta da ake kira bakon dauro wadda wasu ke kira kyanda.

“Na fara waka ne a 2007, lokacin siyasa ta zo, a lokacin ina kokarin nema wa kaina mafita ” a cewarsa.

Malam Yahaya ya bayyana cewa babban kalubalen da ya fuskanta lokacin da ya fara waka shi ne yadda ake nuna masa cewa shi nakasasshe ne kuma mabaraci

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan