Ni Ba Faɗakarwa Na Ke Ba – Jarumi Ali Nuhu

75

Fitaccen Jurumin finafinan Hausa nan na Kannywood wanda ake cewa SARKI wato Ali Nuhu Muhammad ya ce shi ba fadakarwa ya ke ba, kuma bai taba cewa ya na fadakarwa ba. Jarimin ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan Radio Express Kano, ga yadda hirar ta gudana:

Tambaya: Daga karshen karshen 2019 har zuwa yanzu akwai wasu Fina-finai da kai ka ke bada Umurni zaa ga cewa akwai wasu kebantattun jarumai da kake sanyawa a Finafinanka irinsu Umar M. Sharif da Maryam Yahya da Hassana Muhd da sauransu, wasu suna cewa me yasa ba za ka baiwa wasu jaruman dama ba?

Ali Nuhu: Wato Abu daya da na sani shi ne tun da aka kafa masana’artar finafinan Hausa baa ta ba yin wani Darakta ba wanda yake Promoting din jarumai maza da mata ba kamar ni, idan kuma har zaa yi wannan korafin to akwai matsala kenan… domin akalla mata 12 zuwa 13 na yi promoting maza 9 zuwa 10 na yi promoting suka zama Jarumai. Sannan akan magana aiki kuma ya kamata mutane su gane ko a Fim din FKD ne idan ni Ali Nuhu bai dace da role din ba, ba za a saka shi ba, kwana nan nan na kallama wani sabon fim mai suna ‘Bana Bakwai’ ka ganni a ciki? Babu ni a ciki saboda babu role din da yi a ciki.

Tambaya: Wace shawara za ka bayar don bunkasa wannan harka ta Fim?

Ali Nuhu: Abu na farko shi ne duk wanda yake ganin yana da hanya da zai iya nemo hannun jari don bunkasa kasuwancin finafinan to yayi, domin kasuwancin Fim din shi ya fi akan yawan yin fim, in ka yi fim din ina zaka kai?

Kuma wani lokaci za ka ji mutane suna cewa suna cewa fadakarwa mu ke yi, abinda na ke so mutane su gane shi ne mai yin Fim ba malami bane mai koya maka tarbiya, aa shi nishadantarwa ya ke ba malami ba ne mai koya maka tarbiya, mutum ne wanda ya ke nishadartar da kai, amma a cikin wannan nishadantar da kai da ya ke kana iya samun sakonni na wasu abubuwa na gyran halayya, amma fa ba malami bane, za ka ji ana cewa kuna cewa kuna fadakarwa; ni na bude baki na ce maka ina fadakarwa?

Daily Nigeria

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan