Saudiyya Za Ta Fassara Huɗubar Ranar Arfa Zuwa Hausa

5

Shugaban Hukumar Kula da Masallatan Makka da Madinah Masu Alfarma, Abdurrahman bin Abdulaziz Al-Sudais, ya bada umarnin a yi amfani da harshen Hausa wajen fassara Huɗubar Ranar Arfa.

Sheik Al-Sudais ya sanar da haka ne a yayin taron manema labarai na shekara-shekara na aikin Hajjin 2020 ranar Alhamis.

Ya ce an ƙara yawan harsunan da za a yi amfani da su wajen fassara Huɗubar Ranar Arfar daga biyar zuwa 10, kamar yadda jaridar Intanet, Kano Focus ta rawaito.

Sheikh Al-Sudais ya ce harsunan su ne Hausa, English, Malay, Urdu, Persian, French, Chinese, Turkish, Russian da Bengali.

Za a samu huɗubar a kan manhajar Arafat Sermon da kuma dandalin Manarat Al-Harmain.

Sheikh Al-Sudais ya yi nuni da cewa wannan aiki shi ne mafi girma a duniya, kuma Masarautar Saudiyya a shirye take wajen ci gaba da haɗa saƙon Musulunci ga tarin jama’a

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan