An Buɗe Kantin Hirar Mutuwa Na Farko A Birnin Legas

114

Kantin, wani taro ne na wata-wata da mutane ke zama su ci kek, su sha shayi kuma su yi hirar mutuwa.

Mai kantin, Hope Ogbologugo ta ce yana taimaka wa mutane su kara sanin kimar rayuwa.

A cewar Hope “Mutane na matukar tsoron yin maganar mutuwa, kamar idan suka yi maganar mutuwa to tabbas za su mutu. Amma ko mun tattauna batun mutuwa ko ba mu tattauna ba, ai za mu mutu.”

Ta ce kafin ta bude kantin mutuwar, wanda irinsa ne na farko a Afirka ta yamma ba ta iya magana a kan rasuwar mahaifiyarta. Ta ce, duk da dai har yanzu tana kukan mutuwar mahaifiyar, amma tana iya yin hirar mutuwar da mutane.

Kantin hirar mutuwa an yi shi ne a matsayin wurin da mutane za su je domin rage radidin rashin da suka yi.

Wani ma’aikacin cibiyar raya al’adun Birtaniya, Jon Underwood ne ya kafa kantin hirar mutuwa na farko a shekarar 2011, amma sai dai an bude kantin ne irinsa na farko a jihar Lagos

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan