Na Ɗauki Nauyin Karatun ‘Ya’yan Fulani 74 Zuwa Turkiyya- Ganduje

140

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa a lokutan baya gwamnatinsa ta ɗauki nauyin ‘ya’yan Fulani 74 zuwa Turkiyya don so koyo yadda ake sarrafa madara.

Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Asabar a lokacin ƙaddamar da Gidajen Rugag 200 na Fulani a ƙauyen Ɗansoshiya dake ƙaramar hukumar Ƙiru a jihar Kano.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta gina dam mai cin lita miliyan huɗu don amfanin Fulani makiyaya waɗanda ba za su iya fita neman ruwa ba.

A cewar Gwamna Ganduje, ana gayyatar Fulani makiyaya daga dukkan faɗin Najeriya su zo Kano su ci moriyar sabon shirin gwamnatinsa na Gidajen Ruga.

Ya lura da cewa gidajen suna da dukkan kayayyakin more rayuwa da suka haɗa da ruwa, wuraren kiwo, injinan sarrafa madara da kasuwanni.

Gwamna Ganduje ya nuna damuwa bisa yadda makiyaya suka daɗe suna shan wahala, makiyayan da, a cewar sa, sun sha baƙar wahala a Najeriya ta hanyar rasa rayuka, sata, sace shanunsu da sauransu.

Gwamna Ganduje ya tunatar da cewa ba a san Bafulatanin asali da tayar da hankali ba, amma saboda wahalar da ake zargin an jefa su a ciki, ana tilasta musu ɗaukar fansa.

“A yau sai ka ga Bafulatani yana yin fashi, garkuwa da mutane da sauran munanan ayyuka, saboda haka akwai buƙatar kafa Gidajen Ruga sosai da sosai”, in ji shi.

Ya ce duk abinda ya jawo haka shi ne galan ɗin madara ya fi galan ɗin man fetur tsada, abinda a fili yake nuna cewa Bafulatani ba talaka ba ne, ba kuma wawa ba ne.

“An lura cewa mafiya yawan makiyaya masu riƙe da makamai masu hatsari sun zo ne daga Mali, Kamaru da sauran ƙasashen Afirka”, ya ƙara da haka.

Da yake jawabi a madadin Fulanin da suka amfana, Sakataren Ƙungiyar Miyetti Allah ta Jihar Kano, Zubairu Ibrahim, ya yaba wa Gwamnan bisa cika alƙawuransa game da aikin Gidajen na Ruga.

Ya tabbatar wa da Gwamnan cewa za su yi amfani da gidajen yadda ya dace.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan