Ranar 13 ga watan Yunin shekarar 1942 ne aka haifi janar Abdussalam Abubakar mai ritaya a garin Minna na jihar Naija, kimanin shekaru 78 da su ka wuce.
Yayi karatun Firamarinsa a makarantar Native Authority a garin Minna, ya kuma yi karatun sakadiransa a makarantar Provincial Secondary School dake Bida da ga karshe kuma yaje makarantar Technical Institute, daka Kaduna, bayan wannan ne kuma ya shiga aikin soji.

Janar Abdussalam ya jagoranci dakarun sojin Najeriya a Labanon kuma daga bisani ya sa mu mukamin babban hafsan tsaro.
Janar Abdussalam Abubakar shi ne shugaban ƙasa na 11 a jerin wadanda su ka mulki ƙasar nan.
Ana ganin janar Abdussalam Abubakar ya taka rawar gani, la’akari da yadda ya miƙawa farar hula mulkin ƙasar nan. Inda ake yi masa kallon jan gwarzo.

Janar Abussalam na da mace daya Mai sharia Fati da ‘ya ‘ya shida.