An Sanya Ranar Dawowa Gasar Cin Kofin Share Fage Ta Nahiyar Afrika

76

Rahotanni da suke fitowa daga shelkwatar hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afrika wato CAF, na nuni da cewar hukumar ƙwallon ƙafan ta Afrika ta bayyana lokacin daza a dawo domin ci gaba da fafafata wasannin share fage na neman cancantar buga gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Inda hukumar ta ayyana watan Oktoba amatsayin lokwcin daza aci gaba da buga wasannin saidai ba a tsayar da rana ba acikin watan na Oktoba inda za a fafata wasanni rana ta uku dana rana ta huɗu wanda tun a watan Maris akaso fafatasu amma cutar nan ta Coronavirus ta hana.

A watan Nuwamba kuma za a fafata wasanni na biyar dana shida domin samun jerin ƙasashen dazasu fafata gasar cin kofin nahiyar Afrika daza ayi a nan gaba, wanda a gasar da aka fafata a baya ƙasar Algeria ce ta zamo zakara.

Amma hukumar ƙwallon ƙafan ta nahiyar Afrika ta bayyana cewar zata nemi shawarwarin masana lafiya yayin gudanar da wannan wasa na share fagen fafata gasar cin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afrika.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan