Japan Ta Janye Daga Karɓar Baƙuncin Gasar Cin Kofin Duniya Ta Mata

85

Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Japan ta bayyana aniyarta ta janyewa daga Karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya ta mata daza ayi a shekarar 2023.

Hukumar ƙwallon ƙafan ta ƙasar Japan ta bayar da sanarwar ne a jiya Litinin inda ‘yan kwanaki ne suka rage azabi ƙasar daza ayi wannan gasa inda za ayi wannan zaben aranar Alhamis.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya dai wato FIFA tana ganin ƙasashen New Zealand/Aistalia ne akan gaba inda kuma ita ƙasar ta Japan ake ganin itace zaɓin hukumar ƙwallon ƙafan ta duniya ta biyu.

Babban dalilin dayasa Japan ta janye shine tace za ayi gasar guje-guje da tsalle-tsallen a shekara mai zuwa sannan shekaru biyu masu zuwa suce zasu karbi baƙuncin gasar ta mata ta duniya, inda sukace hakan bazai yiwwuba shiyasa suka janye.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan