Nan ba da jimawa gwamnoni 10 za su bar jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC – Yahaya Bello

68

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya ƙaryata cewa akwai rikici a jam’iyyar APC, yana mi cewa kimanin gwamnonin PDP 10 ne za su dawo APC nan bada jimawa ba.

Gwamnan ya faɗi haka ne a lokacin da ake zantawa da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a.

A cewar sa, matakin rushe kwamitin aiki na jam’iyyar da sauran matakan da aka ɗauka a taron majalisar zartaswar ja9a ranar Alhamis ya ƙara ƙarfafa jam’iyyar.

Bello ya kuma ƙaryata raɗe raɗin da ake na cewa APC za ta tarwatse da zaran shugaba Buhari ya sauka daga mulki, yana mai cewa masu faɗin hakan sun tafka babban kuskure.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan