Gwamna Badaru ya buƙaci waɗanda su ka buɗe makarantun islamiyya da su sake rufewa

157

Hadakar kungiyar makarantun Islamiyya ta jihar Jigawa ta umarci dukkanin makarantun Islamiyya da suka koma karatu dasu rufe makarantun ba tare da bata wani lokaci ba.

Da yake bayar da umarnin a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a birnin Dutse, shugaban kungiyar Malam Aliyu Ibrahim Sakwaya ya ce hakan ya biyo bayan umarnin da gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayar a jawabinsa na musamman ga al’ummar jihar nan.

Malam Aliyu Ibrahim Sakwaya ya ce kungiyar makarantun Islamiyya mai biyayya ce ga umarnin da gwamnati ta bayar, tare da jaddada cikakken goyan baya ga gwamnatin jiha da ma’aikatan lafiya kan matakan da aka dauka na yaki da cutar covid-19 a jihar nan.

Shima a nasa jawabin Sakataren kungiyar ya yi kira ga gwamnatin jiha data duba halin da Malam suke ciki kasancewar watanni hudu ke nan da rufe makarantun suna cikin damuwa saboda rashin biyan Malamansu alawus da kudin hayar makarantun duba da halin da ake ciki na annobar corona virus.

Daga nan ya yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa matakan da take dauka na dakile yaduwar cutar, inda ya yi fatan jama’a zasu kalli lamarin da idon basira domin marawa gwamnati baya ta cimma wannan buri.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan