Kungiyar Kwadago ta gargadi gwamnati ta koma tsohon farashin man fetur

3

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), ta yi fatali da karin farashin litar man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi a ranar Laraba.
Kungiyar ta bakin Shugaban ya Ayuba Wabba, ta gargadi gwamnati ta gaggauta komawa kan tsohon farashi na naira 121.50.

Kungiyar ta na magana ne kan karin kudin fetur zuwa naira 140.80 da naira 143.80.

NLC ta ce ta yi hanzarin neman a janye karin bisa ji da ganin yadda ‘yan Najeriya ke ta korafe-korafen karin da aka yi din.

Tun da farko dai hukumar Tantance Farashin Man Fetur (DPPRA) ce ta bayyana ƙarin farashin man a ranar Laraba din nan a Abuja.
DPPRA ta ce haka za a sha kowace litaran fetur naira 140.80k zuwa naira 143.80k cikin watan Yuli.

Sanarwar ta ce an amimce kowane mai gidan mai ya sayar daidai gwargwadon yadda tsadar man ta kai masa shi har garin da yake sayar da man. Wato daga naira 140.80 zuwa naira 143.80.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan