Mohammed Salah Ya Kafa Tarihi Agasar Firimiyayar Ingila

143

Ɗan wasan ƙasar Masar kuma ɗan asalin nahiyar Afrika wato Mohammed Salah ya kafa tarihi agasar ajin Firimiyayar Ingila kuma tarihin dayakafa shine ɗan wasa na farko daba ɗan asalin ƙasar Ingila ba dayayi saurin kafa irin wannan tarihin.

Salah dai ya shiga jerin ‘yan wasan gasar ajin Firimiyayar ta Ingila dayayi saurin cin ƙwallaye guda 100 agasar ta Firimiya kuma wannan ba ƙaramar nasarabace game da yadda ake fafata gasar ta Firimiya shekara da shekaru.

Salah dai ya bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool wasanni 116 inda acikin wasanninne ya jefa adadin waɗannan ƙwallayen guda 100 kuma Salah yana daga cikin ‘yan wasan da suka taimakawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta lashe gasar ajin Firimiyayar Ingila a karon farko tun bayan da aka sauyamasa suna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan