Sabuwar Kalar Rigar Da Barcalona Zatayi Amfani Da Ita A 2020 Zuwa 2021

169

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcalona ta fitar da kalar sabuwar rigar dazatayi amfani da ita a sabuwar kakar wasa daza’a shiga anan gaba wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 inda kuma nan bada jimawa ba za a fara buga sabuwar kakar wasan.

Wannan kalar rigar da mahukunta ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Barcalona da suka fito da ita tana kama da kalar rigar da Barcalona take amfani da ita ahalin yanzu amma saidai akwai bambamce-bambamce a tada da kuma ta yanzu inda sai mutum ya ƙurawa rigar ido sosai sannan zai gane.

Wasanni guda huɗu ne suka rage a kammala kakar wasannin Laliga ta bana inda daga nanne za a sake sanya ranar fara buga sabuwar kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 inda alokacinne zasuyi amfani da sabuwar kalar rigar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan