Za A Fara Jarrabawar WASCE Ranar 4 Ga Agusta

206

Za a fara Jarrabawar Kammala Babbar Sakandare ta Afrika ta Yamma, WASCE daga 4 ga Agusta zuwa 5 ga Satumba, 2020.

Ƙaramin Ministan Ilimi, Emeka Nwajuiba ya sanar da haka a ranar Litinin yayin taron manema labarai da Kwamitin Yaƙi da COVID-19 na Shugaban Ƙasa yake shiryawa kullum.

Ministan ya ce da zarar an kammala WASCE, za a fara jarrabawar NBC da NTC da Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Makarantun Fasaha, NABTEB ke shiryawa, da kuma Jarrabawar Kammala Sakandare ta Ƙasa, SSCE da Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Babbar Sakandare ta Ƙasa, NECO ke shiryawa.

Dama tun a baya Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ɗaliban shekarar ƙarshe, da suka haɗa da waɗanda za su zana WASCE za su koma makaranta.

Tun a watan Maris aka kulle dukkan makarantu a Najeriya, a wani ƙoƙari na daƙile yaɗuwar cutar COVID-19.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan