Aminu Ado Ya Naɗa Babba Dan-Agundi Sarautar Sarkin Dawaki Babba

101

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya amince da naɗin tsohon Sarkin Dawaki Mai Tuta, Aminu Babba Dan-Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba, kuma ɗan Majalisar Masarautar Kano.

Majiyarmu ta rawaito cewa wannan ya saɓa wa matakin da marigayi mahaifin Sarki Aminu, Sarki Ado Bayero ya ɗauka, wanda ya sauke Mista Dan-Agundi bisa zargin sa da rashin biyayya.

Naɗin Mista Dan-Agundi yana ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da Mataimakin Sakataren Majalisar Masarautar Kano, Sarki Waziri, (Ɗan Rimin Kano) ya aika wa Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji domin amincewa.

Marigayi Sarki Bayero ya sauke Mista Dan-Agundi a 2003 daga sarautar Hakimin Gabasawa, kuma Sarkin Dawaki Mai Tuta bisa zargin sa da rashin biyayya.

An zargi Mista Dan-Agundi da ƙin yin biyayya ga wani umarni marigayi, wanda ya buƙace shi ya gurfana a gaban Sarkin.

Jim kaɗan bayan sauke shi, sai Mista Dan-Agundi ya maka tsohon Sarkin a da kuma Majalisar Masarautar Kano a wata Babbar Kotun Jiha don a yi masa adalci.

Alƙalin Babbar Kotun Jihar, Sadi Mato, ya bada umarnin a mayar wa Mista Dan-Agundi muƙaminsa, kuma a biya shi dukkan haƙƙoƙinsa.

Sai dai Majalisar Masarautar Kano ta ɗaukaka ƙara, amma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Jihar.

Majalisar Masarautar Kanon, a ƙarƙashin Sarki Sanusi II, ta shigar da ƙara a Koton Ƙoli, inda take ƙalubalantar hukuncin kotunan biyu.

A ranar 5 ga Yuni, 2020, shekara shida bayan rasuwar marigayi Sarki Ado Bayero, Kotun Ƙolin ta tabbatar da hukuncin Sarki Ado Bayero na sauke rawanin Aminu Babba Dan-Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Mai Tuta, kuma Hakimin Gabasawa.

Aminu Ado ko Majalisar Masarautar Kano ba su yi bayanin dalilin dawo da Mista Dan-Agundi ba a matsayin ɗan Majalisar Sarki kuma Sarkin Dawaki Babba ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan