Attajiri A. A Rano zai fara hada-hadar sufurin jiragen sama

7

Hamshaƙin dan kasuwar man fetur da ke jihar Kano, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano ya shirya tsaf domin fara kasuwancin sufurin jirage. Auwalu Rano wanda aka fi sani da A. A Rano zai fara harkar sufurin jiragen da sunan Rano Air Limited.

Tuni dai shirye-shirye neman lasisi daga hukumar kula zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasa NCAA ya yi nisa, wanda hakan zai bayar da damar tsara jadawalin yadda fasinjoji da kuma daukar kaya za su kasance.

Mun yi ƙokarin jin ta bakin Alhaji Auwalu Rano abin ya ci tura, sai dai wani makusancinsa ya tabbatar mana da cewa A.A Rano ya baiwa harkar sufurin jiragen saman muhimmancin gaske.

Turawa Abokai

3 Sako

  1. Tarabiyya daga Iyalai da Dange a Kasar Hausawan Rano
    Wannan wata Babbar hanya ce da Hausawan kasar Rano suke bi wajen koyawa yara Kyakkyawar Tarabiya don su tashi da halayen kyawawa, Idan yara suka tashi babu wannan Tarabiya to rayuwarsu takan kasance cikin muni da rashin jin dadin rayuwa. Hakika Hausawan kasar Rano sun kan koyawa kananan yara tarabiyyar rayuwa wato ma’anar yadda zasu tashi su zamo mutane na gari a rayuwarsu, tun yara suna kanana ake nuna musu matsayin na gaba dasu kamar Iyaye da Yayye da sauran manya yadda zasu dinga yi musu biyayya da kuma yadda zasu dinga yin gaskiya a cikin zancensu. Da kuma yadda zasu ke gudun masu cin mutuncin Iyayensu da Yayyensu da Manyansu. Wannan Kadan ne daga cikin kyawawan Halayen Hausawan Kasar Rano, a karshe Ina Addu’a Allah Ubangiji ya jikan Iyayenmu da Sarkunnanmu da Malamanmu da sauran Alummar Musulmai Ameen By: A.M.Rano

  2. Aslm da farku INA rukun Allah ya kareshe ya yimai kariya tah alheri ya bashe ikun rike gaskiya da ammana Allah karemai dukiyatai ameen kuma dun Allah ya taimakama talakawa Allah she bashe ikun taimakamun

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan