Mahaukaciyar guguwar Hana ta afkawa birnin Texas da ke ƙasar Amurka

3

A ranar Asabar guguwar Hanna, ta farko a shekarar 2020 daga tekun Atlantika ta afka wa gabar tekun Texas, daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar annobar coronavirus a Amurka, inda ta taho da ruwan sama mai karfin gaske, tare da ambaliya mai matukar hadari.

Guguwar dake rukuni na daya ma’auninta ta taho da iska mai gudun mil 90 ko kilomita 145 a cikin sa’a guda, yayin da ta isa gabar ruwan tsibirin Padre da misalin karfe 10 na dare agogon GMT.

Hotunan bidiyo sun nuno yadda guguwar ta kayar da bishiyoyi, da kuma gine gine da ta lalata.

Wasu masu motoci sun hau kan hanyoyin da ambaliyar ta rufe, yayin da hukumomi ke shirya wa mahaukaciyar guguwar da ake sa ran za ta isa wasu yankunan jihar a kowane lokaci daga yanzu.

Babu rahoton mummunar rauni ko salwantar rayuka a inda wannan guguwar ta afka wa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan