An Ƙona ‘Yan Fashi 3 Ƙurmus A Oyo Bayan Sun Kai Hari A Banki

124

A ranar Laraba ne wasu fusatattun matasa suka ƙona wasu ‘yan fashi uku da suka kai wani hari da bai yi nasara ba a First Bank da yake Okeho a ƙaramar hukumar Kajola a jihar Oyo.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya tattaro cewa ‘yan fashin, waɗanda suke ɗauke da bindigu ƙirar AK47 da abubuwan fashewa, sun yi yunƙurin yin fashi a bankin da yake Okeho, amma sai ‘yan sanda da mafarautan yankin suka fi ƙarfin su, kamar yadda jaridar Intanet, TheEagleOnline ta rawaito.

Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo, SP Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari, yana mai cewa al’amarin ya afku ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin Laraba.

Mista Fadeyi ya ce: “Da misalin ƙarfe 4:58 na yamma, an samu fashin banki inda wasu muggan ‘yan fashi ɗauke da makamai waɗanda suka zo a cikin bas mai cin mutum 18 suka kai hari First Bank, da yake Okeho a ƙaramar hukumar Kajola ta jihar Oyo, da nufin yin fashi.

“‘Yan fashin waɗanda suka samu suka shiga bankin sun yi amfani da abubuwan fashewa da bindigu ƙirar AK47 suka harba don lalata ƙofar tsaro ta bankin.

“Yadda jami’an ‘yan sanda, ‘yan bigilanti da mafarauta suka tunkari fashin ya haifar da ɗa mai ido.

“Sakamakon haka, lokacin da aka cafke uku daga cikin ‘yan fashin bayan bas ɗinsu mai cin mutum 18 ta yi hatsari inda ta yi adungure, sai wasu fusatattun matasa suka ƙona su ƙurmus lokacin da suka yi yunƙurin guduwa daga inda aka yi hatsarin.

“Nan da nan Kwamishinan ‘Yan Sanda, Nwachuckwu Enwonwu, ya shawo kan wannan mummunan al’amari, ya kuma bada umarnin cewa dukkan Ƙwararrun Jami’an ‘Yan Sanda da suka haɗa da Rundunar Musamman Mai Yaƙi da ‘Yan Fashi, SARS, ‘Yan Sandan Kwantar da Tarzoma, PMF 72, da kuma jami’an ‘yan sanda daga Rundunar Yanki ta Okeho da Ofishin ‘Yan Sanda na kusa da su fara neman sauran ‘yan fashin da suka gudu waɗanda suka yi wurare daban-daban”.

Mista Fadeyi ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda ya yi Allah-wadai da wannan mummunan al’amari, ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar Oyo cewa ‘yan sanda a shirye suke wajen kare rayukansu kafin, yayin da bayan bukukuwan Salla.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da jin wani tsoro ba daga ko’ina, yana mai cewa ‘yan sanda suna binciken al’amarin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan