Ƙididdiga Akan Ƙungiyoyin Dasuka Lashe Gasar League Ɗinsu

120

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda biyar a manyan league wato gasar rukuni-rukuni ta nahiyar turai da suka haɗar da gasar Serea a da aka kammala adaren jiya da gasar Laliga da gasar Bundes Liga da gasar Firimiyar Ingila da kuma gasar League 1 ta ƙasar Faransa.

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan dasuka zamo zakaru a wadannan manyan gasoshi akwai Real Madrid da Paris Saint Germain da Liverpool da Bayern Munich da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus.

Saidai jaridar Labarai24 tayi nazari akan yawan makin da kowacce ƙungiya ta lashe gasar dashi.

  1. Liverpool ta lashe gasar Firimiyar Ingila da maki 99.
  2. Real Madrid ta lashe gasar Laliga da maki 87.
  3. Juventus ta lashe gasar da maki 83.
  4. Bayern Munich ta lashe gasar da maki 82.
  5. Itakuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain ta lashe gasar da maki 68 duk da ba a kammala gasar ba, inda ta lashe a iya wasanni 27 databuga.
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan