Masallacin Al-Aqsa: Masallaci Mai Muhimmanci Ga Musulmi, Yahudawa, Kiristoci

107

Masallacin Al-Aqsa masallaci ne mai ɗimbin tarihi a duniya. Shi ne alƙiblar Musulmi ta farko kafin Allah Ya bada umarnin canza alƙiblar zuwa Masallacin Harami na Makka.

Musulmi, Yahudawa da Kiristoci suna danganta kansu da wannan masallaci saboda muhimmancisa.

Ga wasu abubuwa takwas da jaridar “Musulim Hands UK” ta kawo game da wannan masallaci, Labarai24 kuma ta fassara don amfanin masu karatu.

 1. Ba Masallaci Ɗaya Ba Ne Kawai
  Akwai masallatai da yawa a wajen da muka sani da Masallacin Al-Aqsa. Muna tunanin Masallacin Al-Aqsa shi ne ginin da yake a kwanar Kudu mai nisa. A zahiri, wannan shi ne Masallacin Alƙibla- an kira shi haka ne saboda shi ne mafi kusa da Alƙibla. Gaba ɗaya harabar Masallacin Al-Aqsa ne ana ce mata “al-Haram as-Sharif”.
 2. Shi Ne Kaɗai Masallacin Da Aka Ambata A Ƙur’ani, Banda Masallacin Ka’aba

“Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya yi tafiya da bawanSa da daddare daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Al-Aqsa, wanda Muka yi albarka a kewayensa. Haƙiƙa Shi ne Mai ji, Mai gani. (Qur’an 17:1).

 1. Asalin Hasumiyar “Dome of The Rock” Daban Take
  Khalifa Umayyah Abdul Malik ibn Marwan shi ne asalin wanda ya gina Dome Of The Rock. A baya an gina ta ne da katako da tagulla, darma da sauransu. Bayan shekara 1000, Ottoman Khalifah, Suleyman the Magnificent, ya gina hasumiyar da muke gani yanzu.
 2. Harabar Masallacin Maƙabarta Ce
  Kodayake ba a da bayanan da wa da wa aka binne a wannan waje, akwai Annabawa da yawa da Sahabban Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare da aka binne a wajen.
 3. An Taɓa Samun Wani Mambari Na Tarihi A Masallacin
  Imad ad-Din Zengi daga zuriyar Zengid na Turkiyya yana da wani mambari na musamman da aka sa a Masallacin Al-Aqsa. Wannan mambari ba kawai yana da kyau ba, an yi shi ne ba tare da amfani da ko ƙusa ɗaya ko gam ba. Sai dai kash! Imad ad-Din bai samu ganin haka ba, amma ɗansa ya cika wannan burin malamin nasa, bayan ‘yantar da Jerusalem a karo na biyu a tarihin Musulunci, ya kafa mambarin.
 4. An Taɓa Mayar Da Harabar Masallacin Bola

Lokacin da Romawa suka kori Yahudawa daga Jerusalem, sai Romawan suka riƙa amfani da harabar Masallacin Al-Aqsa a matsayin bola. Lokacin da Sayyidna Umar ya buɗe birnin ga Musulmi, sai ya share sharar da hannayensa. Ya kuma kawo ƙarshen korar da aka yi wa Yahudawa ta ɗaruruwan shekaru, inda ya ba ‘yan gudun hijira damar dawowa Jerusalem

 1. Al Ghazali Ya Rayu Tare Da Rubuta Littafinsa A Masallacin
  Ɗaya daga cikin shararrun malaman addinin Musulunci, Imam Abu Hamid Al-Ghazali, ya taɓa zama a Masallacin Al-Aqsa inda ya rubuta shararren littafinsa mafi girma “Ihyaa Ulum Al-Din (Raya Iliman Addini). Akwai gini a masallacin da yake nuna ɗakin da ya zauna.
 2. An Taɓa Ƙona Shi Ƙurmus
  A 1969, aka ƙona Masallacin Qibla gaba ɗaya. Tuntuni aka sake gina masallacin. Wannan al’amari da bai daɗe da faruwa ba yana nuna muhimmancin kula da wannan waje na uku mafi alfarma a Musulunci.
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan