Motocin Bas-Bas Na Zamani Na Dab Da Fara Aiki A Kano- Kwamishina

140

Ma’aikatar Gidaje da Sufuri ta Jihar Kano ta kammala shirye-shiryen fara aiki da sabbin motocin bas-bas na zamani domin sufuri a ƙwaryar birnin.

Kwamishinan Sufuri, Mahmud Muhammad ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Talata a Kano lokacin da yake duba sabbin motocin a Hotoro, a cewar jaridar The Nation.

Mista Muhammad ya bayyana farin cikinsa bisa matakin aiki da kamfanonin dake aikin samar da motocin suka kai wajen samar da su, samar da tikiti na Intanet da sauran kayayyakin da ake buƙata.

“Gwamnatin jihar Kano za ta tallafa wajen samar da dukkan kayayyakin da suka wajaba don kammala aikin cikin nasara”, in ji shi.

Ya yi kira ga masu kamfanin da su haɗa kai da ma’aikatar Sufuri ta Jihar Kano wajen bunƙasa tsarin sufuri na zamani a jihar.

Gwamnatin jihar Kano ta sanya hannu a kan wata Yarjejeniyar Fahimtar Juna, MoU da kamfanonin Messrs Shaanxi Company da Zoec Constructions Nigeria Ltd don samar da bas-bas da wuraren tsayawarsu da nufin zamanantar da tsarin sufuri a birnin Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan