Gwamnatin jihar Kano ta bayar da hutun shekarar musulunci

145

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana gobe alhamis a matsayin ranar hutun sabuwar shekarar musulunci ta 1442 bayan hijirar Annabi SAW.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci al’ummar musulmi a jihar Kano da su yi amfani da hutun wajen yiwa jihar Kano addu’ar samun zaman lafiya da bunƙasar arziƙin jihar.

Haka kuma Gwamnan Ganduje ya taya al’ummar jihar Kano murnar zagayowar sabuwar shekarar ta musulunci, tare kuma da yin addu’ar neman Allah ya ye matsalar da ake fuskanta ta tabarbarewar tattalin arziki wanda annobar korona ta haifar, ya kuma ja hankalin al’ummar jihar Kano da su ji tsoron Allah a dukkanin al’amuransu.

A ƙarshe ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen bunƙasa cigaban al’ummar jihar Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan