Bai Kamata Lauyoyi Su Janye Gayyatar Da Suka Yi Wa El-Rufa’i Ba- Sanusi

135

Tsohon Sarkin Kano da aka tsige, Muhammad Sanusi II, ya ga baiken Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, NBA bisa janye gayyatar da ta yiwa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Elrufa’i a taron da ta za ta yi.

Tsohon Sarki Sanusi, wanda yake ziyararsa ta farko a jihar Kaduna tun bayan ƙaurasa zuwa garin Ikko bayan tsige shi daga karagar mulki a watan Maris ya ce ya karanta zargin da Ƙungiyar ta Lauyoyi ta ke yi wa wa Gwamnan, amma bai ga cikekken dalilin haka ba.

“In an ce mutum ba ya kula da tsarin doka, mene takamaiman laifin? A wane irin yanayi ne yake sakaci da rikicin Kaduna? Kowa na faɗin komai, na kan iya cewa mutum na rashawa, me haka ke nufin, hakan ba komai ba ne”. In ji Sarkin.

Sarkin da aka yi wa masauki a Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna, ya ce ba ya son alaƙanta maganar da Ƙungiyar Lauyoyi tunda ‘yan Najeriya sun faɗi ra’ayinsu, amma ya kamata ƙungiyar ta bar Gwamnan ya zayyana mata dalilan zargin da ta yi masa, maimakon soke gayyatar ta sa.

“Sai ku ƙalubalanci abin da kuka ga yayi ba daidai ba, sai ku koyi wani abu daga gare shi, shi ma ya koya daga gare ku, amma soke gayyatar sa ba hanyar ci gaba ba ce ga mutanen dake son ci gaba”, a cewarsa.

Tsohon sarkin wanda babban aminin gwamnan ne ya ce tashin-tashinar dake afkuwa a Kaduna ta daɗe kuma wannan shi ne karon farko da Gwamna El-Rufa’i ya zage danste domin shawo kan matsalar.

“Duk Arewa ana fama da irin waɗannan fitintunu ne saboda akwai waɗanda ke amfanuwa daga rikice-rikicen, mun yi nasarar raba kawunanmu mu ta nasabar ƙabilanci da addini, ganin an samu mutum da zai tsaya bisa adalci da bin haƙƙin ɗan Adam. Amma mutanen da ba su son a aiwatar da haka za su daƙile samo maslaha”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan