Alhakin samar da tsaro a Najeriya ba a wuyan Buhari ya rataya kaɗai ba – Sabo Nanono

140

Mininistan harkokin noma na ƙasa Muhammad Sabo Nanono ya ƙalubalanci gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi kan matsalar tsaro a Najeriya.

A wata zantawa da ministan yayi da sashen Hausa na Radio France International kan yadda matsalar tsaro ta shafi ɓangaren noma.

Ministan ya ce “magana ta Allah da Annabi ba gwamnatin tarayya ce ta ke da haƙƙin tsaron wannan abu kawai ba, gwamnatocin jihohi ƙananan hukumomi, in ka tafi ƙasa har Dagatai da masu unguwanni, ya aka yi suka sake suka bar wannan yanayi na tsaro ya zama abin da ya zama, amma kowa ya tashi sai ya ce gwamnatin tarayya”.

“Eh gwamnatin tarayya tana da haƙƙin ta tsare rayuwa na jama’a, amma ai su waɗannan da suke kusa da waɗannan mutanen su ya kamata tun da farko ma su fara maganar cewa muna ganin muna da matsala a kan waɗannan abubuwan”.

Sabo Nanono ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya tana iya ka ƙoƙarinta wajen bunƙasa noma da samar da abinci a ƙasar nan.

Karuwar hare-hare da sauran aiyukan ta’addanci na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan Najeriya ke ikirarin aniyar murkushe ‘yan bindiga dadi da sauran masu tayar da kayar baya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan