Chelsea Ta Sayi Thiago Silva Daga Paris Saint Germain

188

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea dake birnin London na ƙasar Ingila ta tabbatar da sayen ɗanwasan bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain kuma ɗan asalin ƙasar Brazil wato Thiago Silva.

Silva dai yana da shekaru 34 ahalin yanzu inda tun a watanni 3 dasuka gabata PSG ta tabbatar masa da cewar yaje ya nemi sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa duba da cewar sunason sukawo sababbin jini.

Chelsea dai na tayin cefane domin ganin cewar sunyi zarra a gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila da kuma gasar zakarun nahiyar turai wato sabuwar kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 duka a ƙarƙashin mai horas wa wato Frank Lampard.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan