Aokigahara: Daji Da ‘Yan Japan Ke Zuwa Don Su Kashe Kansu

101

“Yi tunani sosai game da ‘ya’yanka, iyalinka, kuma “Rayuwarka aba ce mai tsada daga iyayenka”.

Waɗannan su ne kalmomin gargaɗi da za ka gani kafin shiga Dajin Aokigahara dake Japan, dajin da aka fi sani da “Dajin Kashe” Kai a faɗin duniya. Ko ka taɓa jin Dajin Aokigahara na Japan? Idan ba ka taɓa ji ba, bari in faɗa maka cewa wannan koren daji mai kyan gani ba wajen shaƙatawarka ba ne a yawonka na safe, wannan dajin yana da mummunan tarihin kasancewa wuri na biyu mafi shahara da ake kashe kai a duniya(na farko ita ce Gadar Golden Gate).

Jaridar Times of Indian ce ta wallafa wannan rubutu da harshen Turanci, Labarai24 kuma ta fassara don amfanin masu karatu.

Na so a ce wannan abu wasa ne, amma wannan ita ce gaskiya game da wannan kyakkyawan daji mai matuƙar ƙayatar da idanu a Japan, wanda bai wuce tafiyar sa’o’i biyu ba daga Tokyo, babban birnin ƙasar.

Inda Dajin Yake

Dajin Aokigahara ko kuma Dajin Kashe Kai yana Arewa Maso Gabashin Dutsen Fuji. Ya mamaye wuri da ya kai faɗin sikwaya kilomita 35. Dajin Aokigahara cike yake da bishiyu da ganyayyaki, shi yasa ana kuma ce masa “Tekun Bishiyoyi”.

Ɓata a wannan wuri abu ne mai sauƙi, kuma fitowa kusan abu ne da ba ya yiwuwa saboda duhunsa.

Camfi Da Ake Faɗa Game Da Wannan Daji

Ana cewa wannan daji shi ne gidan yūrei, wanda a cewar gargajiyar Japan yana nufin fatalwa. A bayanan hukuma, an samu gawarwaki 105 a wannan daji a shekarar 2003, kuma mafiya yawansu sun ruɓe sosai, ko kuma dabbobin daji sun cinye su.

Mafiya yawan bokayen Japan sun yi imanin cewa waɗannan kashe-kashen kai sun shiga cikin bishiyoyin Aokigahara, abinda yake haifar da abubuwan al’ajabi.

Dukkan abubuwan fasahar zamani da na’urori kamar wayoyin hannu ba sa aiki a cikin wannan daji saboda tarin mayen ƙarfe da girgizar ƙasar dutse ta haifar a yankin.

Agoguna masu nuna jiha ba sa aiki yadda ya kamata, kuma suna nuna jiha ba daidai ba, wayoyi kuma ba sa karɓar alamu. Saboda haka yanzu ka san abinda yasa fitowa daga dajin ke gagara, saboda ba abinda yake aiki a dajin.

A cewar mutanen Japan, bai kamata a bar gawarwakin mutanen da suka kashe kansu ba a daji, saboda haka ma’aikatan dajin sukan dawo da su, ana ajiye waɗannan gawarwaki a cikin wani ɗaki na musamman a caji ofis na ‘yan sanda dake kusa da dajin.

Ana yin haka ne saboda mutane sun yi imanin cewa wannan mummunan abu ne ga waɗanda suka kashe kansu, kuma rayukansu suna kuka, suna ihu, suna motsa jukkunansu.

Waje Ne Na Masu Sha’awar Doguwar Tafiya A Ƙasa Da Masu Neman Suna

Sakamakon kyan da yake da shi, ɗaruruwan masu sha’awar doguwar tafiya a ƙafa da masu neman suna suna ziyartar wannan daji don su ga irin kyan da Dutsen Fuji yake da shi.

Haka kuma, waɗanda suke ziyartar wannan daji don yawon buɗe ido ba sa zuwa su kaɗai, suna kuma tahowa da tif na roba a matsayin wata alama don guje wa ɓata.

Sukan yi wa bishiyoyin alama da zare ko tif su ɗaure a tsakanin bishiyoyin, hakan yana taimaka musu su gane hanya idan za su dawo. Haka kuma, a wannan daji akwai bishiyoyi da ba ko’ina a ke samun su ba waɗanda sun fi shekara 300 a raye.

Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Kafin Ka Ziyarci Dajin

Kar ka bar hanya, kuma koyaushe ka bi alamomi.
Kar ka shiga kai kaɗai.
Ka tafi da tif na roba ko zare a matsayin alama kodayaushe.
Kar ka je ziyara da daddare.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan