Rakitic Yayi Bankwana Da Barcelona

141

Za a iya cewa anci moriyar ganga kuma anyar da kwaurenta domin kuwa ayanzu haka ɗanwasa Ivan Rakitic yayi ban kwana da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ayammcin jiya Talata domin komawa wata ƙungiyar.

Tunidai za a iya cewa Rakitic ya koma inda ya fito wato Sevilla inda daga can Barcelona ta sayishi a shekarar 2014 inda ya kwashe shekaru 6 kenan tare da Barcelona inda ya bugamusu wasanni 200 yasami nasarar jefa ƙwallaye guda 25.

Ayanzu ta tabbata cewar ungulu ta koma gidanta na tsamiya kenan inda daga shekarar 2011 zuwa 2014 Rakitic ya bugawa Sevilla wasanni 127 kuma yajefa ƙwallaye guda 27.

Shidai Rakitic ya lashe kofuna da dama tare da Barcelona ciki harda kofin Laliga da Copa del Rey da kuma gasar zakarun nahiyar turai dadai sauran wasu kofunan masu muhimmanci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan