Na Rage Farashin Litar Man Fetur A Gidajen Maina Don Sauƙaƙa Wa Talaka- A.A. Rano

133

Shugaban Kamfanin A.A Rano Nigeria Limited, Auwalu Ali Rano, ya bayyana dalilin da yasa yake siyar da litar man fetur N158 a dukkan gidajen mansa, duk da ƙarin farashin litar man fetur da aka samu zuwa N160 a dukkan faɗin Najeriya.

Da yake jawabi a wani taron Bada Horo a Kano ranar Laraba, Mista Rano ya ce ya ɗauki wannan matakin ne don rage wa ‘yan Najeriya wahala.

Mista Rano ya ce duk da cire hannu da gwamnati ta yi daga harkar mai a ƙasar nan gaba ɗaya wanda ya haifar da gasa a tsakanin ‘yan kasuwa, kamfaninsa ya yanke shawarar tausaya wa ‘yan Najeriya maimakon cin riba.

Ya ƙara da cewa amma gasar farashin da take a ɓangaren mai tana buƙatar kamfanin mai ya riƙa yin abubuwa da inganci idan yana so a ci gaba da damawa da shi, yana mai ƙarawa da cewa: “Wannan shi ne dalilin da yasa kamfaninmu ya fara ba ma’aikata horo don biyan buƙatun abokan cinikinmu.

“A kodayaushe kamfaninmu a shirye yake don kyautata wa ‘yan Najeriya, abinda aka san shi da haka fiye da shekara 20.

“Idan za ku iya tunawa, a koyaushe muna tare da ‘yan ƙasa ta fuskar wahalhalu da rashin tabbas, saboda haka akwai buƙatar yin irin waɗannan tarukan don kyautata wa kowa da kowa”, in ji shi.

Turawa Abokai

11 Sako

  1. Allahu yasaka maka Da Alkairi AA rano Allah yayi maka sakaiyya dagidan Aljannah bisa gataimakon dakakeyima talakawa

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan