Ya Kamata Buhari Ya Buɗe Boda Ko Talaka Ya Samu Sauƙi- Sheikh Gumi

3

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta buɗe iyakokin ƙasar saboda a samu sauƙi a wahalhalun hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a ƙasar, in ji wani rahoto na BBC Hausa.

Babban malamin, wanda ke zaune a jihar Kaduna dake Arewacin ƙasar, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a faron makon nan.

Malamin ya ce matsalar tattalin arzikin ƙasa abu ne mai wahala ƙwarai da gaske, inda ya ƙara da cewa dole sai gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace.

”Na farko dai bai kamata a kulle boda a lokacin da mutane ke buƙatar abinci ba. Barin boda a buɗe na bai wa manoman duniya damar kawo abincinsu kuma hakan zai sa abinci ya yi araha, domin kowa na so ya sayar.

”Yanzu misali a Thailand ga shi nan sun yi shinkafa jibgi guda amma tana neman ta ɓaci. Ka ga idan suka ga za ta ɓaci kafin akai ga hakan sai su kawo ta da araha. A Amurka mun gani har madara ake zubarwa. To ka kulle boda kuma ba ka da isasshe ba dole a yi ɓarna ai”, in ji shi.

To amma a na ta ɓangaren, gwamnatin ta ce ba za ta budo boda ba a wannan karon.

Sheikh Gumi ya ci gaba da cewa ya kamata gwamnati ta duba batun wutar lantarki tare da rage kuɗin da ta ƙara.
“Ai mun san cewa ruwan Allah ne da na dam suke taimaka wa wajen bunƙsar lantarkin nan.

”Ba wani makuɗan kuɗi ake kashewa a harkar ba, to don me za a tsawwalawa mutane da albashinsu ma bai taka kara ya karya ba.

”Don haka ya kamata a sake lale a tsarin, ba mutane za a ƙuntatawa ba,” a cewarsa.

To sai dai a nata bangaren gwamnatin ta ce tana kashe makudan kuɗaɗe duk wata wajen biyan masu samar da wutar, kasancewar kamfanonin rarraba wutar lantarki ba sa iya biyan kuɗin wutar da ake tura musu.

Ana yi wa Dr Gumi kallon wani mai yawan sukar gwamnatin Shugaba Buhari tun kafin ma shugaban ya ɗare mulkin ƙasar, a cewar rahoton BBC Hausa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan