Za Mu Raba Titunan Kano Da Almajirai- Hisbah

14

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta cafke almajirai 648 a birnin Kano daga Fabrairu zuwa yanzu sakamakon karya dokar hana barace-barace ta jihar.

Jam’iin Huɗɗa da Jama’a na hukumar, Lawan Ibrahim, ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a Kano.

Mista Ibrahim ya ce an cafke almajiran ne a yankin Bata, Titin Murtala Muhammad, Asibitin Nasarawa, Titin Railway da Yahuza Suya.

Ya ce an kama maza 16, mata 232.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da kama almajirai masu kunnen ƙashi.

“Za mu raba titunan Kano da almajirai”, in ji shi.

“Tuni an tantance waɗanda aka kama, waɗanda wannan ne karon farko da suka karya wannan doka za a mayar da su ga ‘yan uwansu.

“Waɗanda kuma ba wannan ne karon farko da suka karya wannan doka ba za a maka su a kotu”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan