A shirye-shiryen zaɓukan shekarar 2023, wasu matasa masu goyon tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a tutar jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2019, Alhaji Atiku Abubakar, sun yi sababbin naɗe-naɗe da nufin ganin Atikun ya kai ga nasarar zama shugaban Najeriya a zaɓen shekarar 2023.
Sanarwar naɗe-naɗen na ƙunshe ne a cikin takardar da mataimaki na musamman akan harkokin matasa ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Ambasa Aliyu Bin Abbas ya sanyawa hannu.

Ambasada Aliyu Bin Abbas ya ce sun yi naɗe-naɗen ne domin ganin an samar da shugabanci nagari a ƙasar nan.

“Najeriya ƙasa ce wacce take cike da matasa masu ƙwarewa waɗanda suke sadaukar da kawunansu wajen nuna ƙwarewasu da nuna ƙwazo a wajen shugabanci nagari wanda hakan zai haifar da Ɗa mai ido”
“Haka kuma a yau mun zaƙulo matasa masu kishi da fatan ganin an samu shugabanci nagari a Najeriya, da nauyin jagorantar wannan tafiya ya rataya a wuyansu” In ji Ambasada Aliyu Bin Abbas


“A bisa wannan dalili ne nake gabatar da matasa ƴan kishin ƙasa, masu jajircewa tare da ƙudiri mai kyau da su ka fito daga shiyyoyin siyasar ƙasar nan guda 6 da mu ke da su, wanda za su yi aiki tuƙuru musamman wajen wayar da kan matasa domin ganin an samu shugabanci nagari tare da gina sabuwar Najeriya, kamar yadda mafi yawan al’ummar ƙasar nan ke fata”
- Asiya Balaraba Ganduje ta Kammala Digirin-Digirgir akan harkokin kasuwanci
- Dalilin Da Ya Sa PDP Ta Dakatar Da Anyim Pius Anyim Daga Jam’iyyar
- Rungumar Zaman Lafiya shine mafita tsakanin al’ummar jihar Kano – OXFAM
- Muguntar da Ganduje ya yiwa Kawu Sumaila ce ta janyowa APC faduwa a Kano
- Masu Yin Tattaki Don Nuna Goyon Baya Gare Ni Su Sake Tunani— Abba Gida Gida
Haka kuma Ambasada Aliyu Bin Abbas ya yi wa matasan da aka naɗa fatan alkhairi, tare da jan hankalinsu wajen ganin sun yi aiki tuƙuru domin ganin Alhaji Atiku Abubakar ya kai ga nasarar zama shugaban Najeriya a shekarar 2023.
Waɗanda aka naɗa ɗin sun haɗa da;
Bar Sunday C. Umeha – Sakatare
Comrade Hamza Nasarawa – Shugaban ma’aikata.
Mista Obande G. Obande – Daraktan gudanarwa da shirye-shirye.
Kwamared Rukayya Ahmed Alibe – Mataimakiyar Daraktan gudanarwa da shirye-shirye.
Abdulrahman Etudaiye – Darakta Arewa Ta Tsakiya.
Hon Ibrahim Ali Amsami – Darakta A Shiyyar Arewa Maso Gabas.
Hon. Orishamoluwa Adekunle – Darakta A Shiyyar Kudu Maso Yamma.
Kwamares Isah Abubakar – Darakta A Shiyyar Arewa Maso Yamma.
Kwamared Samuel Eno Okoi – Darakta A Shiyyar Kudu Maso Kudu.
Kwamared Martha Okenna – Darakta A shiyyar Kudu Maso Gabas.
Hon Maciohson Chikone Odev – Daraktan Aiyuka Na Musamman.
Kwamared Shom Akor Fanen – Darakta Harkokin Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kan Al’umma.
Kwamared lorliam Lubem – Mataimakin Darakta Harkokin Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kan Al’umma.
Kwamared Panmak Banwat – Daraktan Ƙididdiga Da Bin Diddigi.
Kwamared Oloja Olanrewaju Temitayo – Daraktan Hulɗa Da Jam’iyyu.
Samira A Usman – Daraktar Mata.
Hon. Haruna Dahiru Bindawa – Daraktan Karɓar Baƙi.
Hon. Muhammed Abubakar – Daraktan Harkokin Waje.