Hukumar Ƙwallon Kwandon NajeriyaTa Ƙulla Yarjejeniya Da Wani Kamfani

4

Hukumar ƙwallon kwando ta ƙasar nan wato NBBF ƙarƙashin shugaban hukumar wato Engineer Musa Kida ta ƙulla yarjejeniya da wani kamfani mai suna Total EP Nigeria dangane da ɗaukan nauyin gasar ta ‘yan rukuni na 1 da kuma rukuni na 2.

An ƙulla yarjejeniyar ne a yammacin jiya inda za a dinga bayar da wasu maƙudan kuɗaɗen da adadinsu yakai kimanin naira miliyan 150 dukkanin gasar guda biyu ta Firimiyar ƙwallon kwando da ake fafatasu a dukkanin kowacce shekara.

Saidai a yayin zaman da akayi tsakanin hukumar da kuma kamfanin an ƙayyade cewar yarjejeniyar ta tsawon shekaru biyar ce inda zata fara daga shekarar nan da ake ciki ta 2020 zuwa shekarar 2025.

Da yake jawabi shugaban hukumar ƙwallon kwandon ta ƙasar nan a jahar Lagos Engineer Musa Kida ya bayyana cewar wannan shine karon farko da aka ɗauki nauyin wannan gasa musamman ƙaramar gasar ta ƙwallon kwando kuma wannan alamu ne da suke nuni da cewar tabbas nan gaba za a iya yiwa wasu kamfanonin allura na cewar suma zasu zuba hannayen jarinsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan