Rashin tsaro na barazana ga Ilimi a Arewacin Najeriya – CITAD

5

Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa ta zamani da cigaban al’umma wato CITAD, ta bayyana takaicinta akan yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a faɗin Najeriya, musamman a yankunan arewa maso gabas da kuma arewa maso yammacin ƙasar nan.

Cibiyar ta CITAD ta ce kalaman ƙiyayya da rikicin ƙabilanci da kuma na addini da su ka raba kawunan al’ummar arewacin Najeriya, haka ma kuma annobar cutar COVID-19 ta jefa harkokin kiwon lafiya da tattalin arzikin yankin arewa cikin mummunan hali.

Tun da farko cibiyar ta CITAD ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Kano, a game da bikin ranar zaman lafiya ta duniya da majalisar ɗinkin duniya ta ware.

A duk shekara, majalisar dinkin duniya na ware ranar 21 ga watan Satumba domin kara fadakar da al’umma muhimmacin zaman lafiya a duniya.

“Hakika akwai matuƙar takaici idan mu ka yi nazari akan yadda ake ƙara samun tashe-tashen hankula a wasu jihohin da ke shiyyar arewa maso gabas da kuma arewa maso yammacin Najeriya, domin a kullum ana samun ƙaruwar ayyukan ta’addanci da kashe-kashe da kuma rikicin manoma da fulani”

“Ana samun ƙaruwar fyaɗe da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, da kona dukiya da kadarorin jama’a da kuma rikici a tsakankanin ma’aurata, da sauran ayyukan da kan haifar da rashin zaman lafiya ” in ji CITAD

A shekarar 2001 Majalisar Dinkin duniya ta sanya ranar ashirin da daya ga watan satumba a matsayin ranar zaman lafiya ta duniya kuma taken bikin bana shi ne jama’a nada yancin a samun zaman

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan