Zargin Zamba Cikin Aminci: Baffa Babba Dan-Agundi ya gaza halartar zaman kotu

156

Kotun majistare da ke Gidan Murtala, ta yi umarnin shugaban hukumar KAROTA Bappa Babba Ɗanagundi ya bayyana a gaban ta a zaman kotun na gaba, ko kuma ta ɗauki mataki a kansa.

Kotun ta sanya ranar 19 ga watan Oktoba mai zuwa domin ci gaba da sauraron shari’ar da masu baburan adaidata sahu suka shigar a kan Baffa Babban.

A zaman kotun na yau Dai Baffa Babba Ɗanagundi bai bayyana ba, inda lauyoyin sa suka ce suna da suka a kan gayyatar da aka yi masa.

Tun da farko dai direbobin baburan adaidata sahun sun yi ƙarar Baffa a kotun, bisa zargin ya yi musu zamba cikin aminci.

Freedom Radio Nigeria

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan