Shekaru 60, Babbar matsalar Nigeria A yau bai wuce son zuciya ba

304

Yau Nigeria ke cika shekaru 60 cif cif da samun yancin kai daga mulkin mallakar turawan ingila. Allah mun gode maka.

A zamanin mulkin mallaka Nigeria da yan Nigeria ababen mallakar kasar Ingli ce, saboda haka duk abun da za a aiwatar sai an je an nemo izini a wurin turawan ingilar, duk da basu suka halicce mu ba, kuma ba umarnin ubangiji bane, munayi musu biyayya kamardai irin biyayyar da mai duka yace mace tayiwa Mijin ta, ko fita zatayi sai ta nemi izininshi, domin fitarta babu izininshi sabawa ubangiji ne.


Yau gashi mun samu hurriya (yancin kai) mun zamanto yan tattu masu iya zartarda duk abun da muke so ba tareda tsangwama ba, ashe dole muyi murna mu taya yan uwanmu ma murna.
Daga samun yancin kai zuwa yau shekaru 60 cif cif, Allah ya kara musu albarka. Nigeria ta zamo kasa mafi yawan al-umma a yammacin Africa, kuma kasa mafi karfin tattalin arziki.

Nigeria tayi girman da ta zarce wasu sa’annin yantakarta.

A yau Dan Nigeria na iya fara karatu daga matakin kolo, yayi firamare yayi sakandare kai har ya zama farfesa ba tare da yafita wata kasa ba, Nigeria ta tasamma zama mai iya ciyar da kanta, an ayyana sojin Nigeria na kasa a matsayin sojin da yafi kwarewa a yakin sunkuru a kaf fadin Africa.Nigeria ta haifawa duniya ‘ya’ya na nunawa sa’a, dan kuwa an samu dan Nigeria mai fede zuciya, an samu dan Nigeria mai wanke kwakwalwa, akwai ‘ya’yan wannan kasa Nigeria a fannoni daban daban na kimiyya da fasaha.To amma duk wani cigaba na da nashi irin gazawar, Alhamdulillahi Nigeria na fuskantar barazanar rashin tsaro, yunwa, karyewar tattalin arziki da rashin tarbiyya, wadda wadannan matsaloli kuma ana jinginasu ne ga son zuciya da cin hanci da rashawa.

Sanin kowa ne hannu daya baya daukar jinka, to yazama wajibi yan Nigeria su tashi haikan wurin ganin sun kwaci yancin kansu daga son zukatansu, domin babbar matsalar Nigeria ayau bata wuce son zuciya.

Allah ka akbarkaci Nigeria.

Comr. Muhammad Auwal Suleiman

Comr. Muhammad Auwal Suleiman

Ya rubuto daga Abuja auwalsuleiman697@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan