Fassarar Taken Najeriya Da Hausa Tare Da Sharhinsa

192

Ku tashi ya ku ‘yan ƙasa
Ku amsa kiran Najeriya
Domin hidimtawa ƙasarmu ta haihuwa
Da soyayya da jajircewa
Wahalar da gwarazan magabatanmu suka sha
Ba za ta tafi a banza ba
Mu yi aiki da zuciya ɗaya
Кasa ɗaya al’umma ɗaya cikin ‘yanci,
Haɗin kai da zaman lafiya

Ya Ubangiji Mahalicci
Ka yi mana jagora a ayyukan kirki
Ka shiryi shugabanninmu zuwa aikata daidai
Ka taimaki matasanmu su san gaskiya
Su girma cikin soyayya da amana
Su rayu da adalci da gaskiya
Har su kai manyan matakai
Su gina ƙasar da amana da adalci za su mamaye

ALƘAWARIN YIN BIYAYYA GA КASA

Na ɗauki alƙawari ga ƙasata Najeriya,
Zan zama mai biyayya kuma mai amana
Zan hidimtawa Najeriya da duk ƙarfina
Zan kyautata haɗin kanta
Zan girmama ƙimarta
Don haka, Allah Ka taimake ni, amin.

КARIN BAYANI:

Jiya Laraba, 30 ga watan Satumba, 2020, ita ce #RanarFassaraTaDuniya. Yau kuma 1 ga Oktoba, ita ce ranar da wannan ƙasa tamu ta Najeriya, mai albarka, amma mara lafiya, ta samu cika shekara sittin (60) a duniya. A gaskiya ta kwana biyu, su Najeriya an sha miya, kuma ana jin jiki! A nan na tuno wasu maganganun Malam Aminu Daurawa, waɗanda na ɗan yi wa kwaskwarima, inda yake kwatanta wani mutum da ya zo duniya, kuma abubuwa suka kacame masa, alhali ga girma ga matsaloli kuma bai yi karatu ba, bai tsaya ya tsara rayuwarsa ba. Malam yakan bayyana wannan mutum da cewa, ga 60 ga 60 ga 60, kuma ba 60 ba 60 ba 60. Me hakan take nufi?

SAMUN ƳANCIN КASA: GA 60 GA 60 GA 60, BA 60 BA 60 BA 60

Da ma fa can akwai Najeriya. Da yawa daga cikin mutane ba ma sa murnar wannan ranar, saboda matsalolin da suke cikin. Mutum ne ya shekara 60, ga shi ya tara ‘ya’ya 60, ga matsaloli 60, amma kuma ba shi da naira 60 (tsurar talaka kenan) ba izu 60 (ba ilimi) kuma ba alheri 60 (cikakken ɗan duniya) a tattare da shi. Wannan kuwa ai sai a ce ya banu ya lalace. A ina zai sa kansa?

A zahirin gaskiya, ni Muhammadu, ina son ƙasar nan, duk da tana tula min tulin takaici. Takaicin ne ma ya sa a wasu lokuta za ka ga mutum ya saki baki yana faɗa wa ƙasar baƙaƙen maganganu, ba don komai ba, kawai don ya huce takaici. Rashin saitin ƙasar nan, ya shafi kowa, daga masu mulki har waɗanda ake mulka, amma masu mulki sun fi rashin imani.

A ranar fassara sai na fara tunanin, shin ko an fassara taken Najeriya da Hausa? Na san tabbas malamanmu sun yi, don ba za a rasa ba. Amma sai na bazama nema cikin sauri. Na ga wani littafi da aka fassara taken Najeriyar a ciki, wanda aka rubuta tun shekarar 1972, amma na kasa samunsa. Don haka sai na koma yanar gizo. A nan na ci karo da wasu fassarori na taken Najeriya daga wajen wasu ‘yan kishin ƙasa kamar: Amina Ibrahim wadda ta sa a shafinta na Facebook ran 2 ga Maris, 2017, Sai kuma wata fassarar da na gani daga Malam Tijjani M. M. (Tijjani Muhammad Musa) shi kuma a 2017, na ga wannan a shafin Tahir Mahmood Saleh da wasu shafukan da yawa. Daga nan kuma sai Bilkisu Ahmed, wadda ita kuma ma’aikaciyar BBC Hausa, ce ita kuma rerawa ma ta yi, a ranar 1 ga Oktoba, 2019.

Gaskiya duk waɗannan fassarori sun burge ni, don haka, sai na yi ƙoƙarin gyaggyara wasu wurare da nake jin ya kamata a gyara, daga cikin abubuwan da na samu, sai na sake inganta fassarorin daidai fahimtata, na kawo su kamar yadda suke a sama. To a yanzu na san abubuwa biyu za su iya faruwa:

1) Wataƙila tun tuni, akwai fassarar da manyan malamanmu suka yi, da wataƙila za ta iya fin wannan inganci. In akwai (na san ma ba za a rasa ba), kuma ta fi wannan inganci, to ni ma ina buƙata.
2) Shi taken ƙasa na kowane ɗan ƙasa ne, don haka, wani zai iya ganin wani ɓangaren akwai buƙatar a fassara shi da wani salon. In kuwa mutum yana da ƙwaƙƙwarar hujja, ta ilimi, to za a iya karɓa a gyara, domin taken na kowa ne.

Taƙaitaccen Sharhi A Kan Taken Najeriya

Кari a kan haka, shi taken ƙasar kansa, ya ƙunshi wasu abubuwa masu muhimmanci. Akwai wata gaɓa da in aka karanto ta, kuma na kalli halin da al’ummar ƙasar nan suke ciki, sai in ji kamar na zubar da hawaye. Wannan gaɓa kuwa ita ce, a Ingilishi inda ake cewa “The labour of our heroes past, shall never be in vain”, wannan kamar wata addu’a ce, wadda take haɗe da ƙarfin halin cewa, dukkanin “wahalar da magabatanmu suka sha, ba za ta tafi a banza ba”! Kuma mu ne ba za mu bari ta tafi a banzan ba. Shin haka abin yake a yau?

A wajen fassarar na haɗa har da ɗaya baitin, domin taken najeriya baiti biyu ne, amma dai ɗaya ake rerawa, kuma shi ya fi shahara. Sannan kuma akwai alƙawarin hidimtawa ƙasa, shi ma na kawo fassararsa. Don haka dai, sai mu cigaba da kishin ƙasa da kuma fatan Allah Ya sa ƙasarmu ta gyaru har ta fi sauran ƙasashe. A ƙarshe, ga na Ingilishin nan na sa a ƙasa, domin mai karatu ya duba kuma ya ƙara dubawa.

Shin ko kuna da wani tsokaci game da taken Najeriya? Zan so in ji!
Godiya mai yawa.

Muhammad Sulaiman Abdullahi malami a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya rubuto daga Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan