Tarihi: Yakubu Gowon ya cika shekaru 86! Abubuwan da ya kamata ku sani game da shi

134

Tarihin Janar Yakubu Gowon

An haifi janar Yakubu Gowon ne a garin Pankshin na Jos jahar Pilato, ranar 19 ga watan Oktoban shekarar 1934.

Janar Gowon ya yi karatunsa a garin Zariya a jahar Kaduna, inda daga bisani ya shiga aikin soji.

Ya samu horan soji a kasar Ghana da Ingila, sau biyu kuma ya yi aiki a kasar Congo a rundunar wanzar da zaman lafiya ta Najeriya a kasar.

Janar Gowon ya yi gudun hijira zuwa kasar Burtaniya, kuma an sauke shi daga mukaminsa bisa zargin sa da hannu wajen kashe wanda ya gaje shi wato janar Murtala Ramat Muhammed a shekarar 1976.

A shekarar 1981 Alhaji shehu Shagari yai masa afuwa, sannan kuma a shekarar 1987, a lokacin mulkin janar Ibrahim Badamasi Babangida akai mayar masa da mukaminsa na soji.

Janar Yakubu Gowon ya yi karatun digirinsa na 3 wato Ph.D a jami’ar Warwick a Burtaniya, ya kuma zama Farfesa a jami’ar Jos.

Mutum ne shi mai haƙuri, gaskiya da kuma riƙon amana sannan kuma jajirtacce a kan duk lamarin da ya saka a gaba.

Janar Gowon, mutum ne mai gudun duniya, wanda Alhaji Tanko Yakasai (2004), ya ruwaito cewa Janar Gowon har ya sauka daga kan kujera mafi girma a Tarayyar Nijeriya bai mallaki gida nasa na kansa ba.

Sannan kuma Farfesa kuma Emeritus a fannin Kimiyyar Siyasa, Elaigwu (1986), ya siffanta shi da cewa cikakken shugaba ne shi abin koyi, mai cike da sauƙin kai tare kuma da tsayuwa ƙyam a kan aikinsa, mai hanƙoron ganin ya ciyar da ƙasarsa da al’ummarsa gaba, mai hangen nesa har ya misalta shi a matsayin Abraham Lincoln ɗin Nijeriya.

Yakubu Gowon Janar ne shi a aikin soja, aikin da ya ɗauki shekaru 21 (1954 zuwa 1975) yana yi, sannan kuma farfesa a fannin ilimin boko. Mayaƙi a filin daga sannan kuma mai bayar da karatu a jami’a.

Zamowarsa Shugaban Ƙasa

Laftanar-Kanar Yakubu Gowon ya zama sabon shugaban Nijeriya a ranar ɗaya ga watan Agusta na shekarar 1966 biyowa bayan juyin mulki haɗe da kisan Janar Aguiyi Ironsi a ranar 29 ga watan Juli na shekarar 1966. Bisa haɗuwar manyan sojojin Arewa a kan shugabantar da shi a maimakon Janar Mohammed Murtala kamar yadda Yakasai (2004), ya ruiwato wanda shi kuma ganau ne ba jiya ba.

Jawabin Farko Na Janar Yakubu Gowon

Ya ‘yan’uwana ‘yan ƙasata, ranar 1 ga watan Agustan shekarar 1966, a matsayina na shugaban Tarayyar Nijeriya, shekarar 1966 ta zama shekarar ƙaddara ga wannan ƙasa, abar alfaharinmu, Nijeriya. An kawo ni wannan matsayin a yau, na ɗaukar ɗawainiyoyin ƙabari kusa na wannan ƙasa bisa sahalewar Majalisar Ƙoli ta Soja a sakamakon abin alhinin da ya afku a safiyar ranar 29 ga watan Julin 1966.

Koma dai menene, kafin na tsunduma cikin batun abin da ya faru a ranar 29 ga wa Juli 1966, zan so na tuna muku abin takaici tare da sanyaya guiwar da ya faru a ranar 15 ga watan Janairun 1966 wanda yake irin wannan ne.

A bisa wasu ƙwararran hujjoji kuma bayyanannu, waɗanda ya zuwa yanzu ba a fito da su fili ba ga jama’ar ƙasa da ma duniya baki ɗaya, an jefa ƙasar nan a cikin annobar da ta shafi dukkan faɗin ƙasa ta hanyar kashe-kashe da kuma aika-aikar da wasu tsirarun sojoji suka ɗauka a kan jama’ar ƙasa. Da wannan, ina nufin wani dandazon wasu ofisoshin sojoji tare da haɗin guiwar wasu fararen hula da suka yanke shawarar hamɓarar da halastacciyar gwamnatin ranar, amma wasu zaƙaƙurai, masu ladabi da biyayya sannan kuma mafiya rinjaye daga cikin rundunar sojoji da ‘yan sanda sun yi wa yunƙurin nasu waigi.

An kira sojoji su karɓi ragamar gudanar da gwamnati har zuwa lokacin da za a dawo da doka da oda. Yunƙurin hamɓarar da gwamnatin ranar an aiwatar da shi ta hanyar kashe wasu shugabannin siyasa tare da wasu manya-manyan sojoji waɗanda mafiya yawan su daga wani yanki na ƙasa suka fito. Firimiya ya rasa ransa a hannun masu juyin mulkin. Amma idan da ba domin ladabi da biyayyar sojojin waɗanda da yawan lamarin ya shafe su da kuma sauran rudunar mayaƙa da ‘yan sanda ba, to da lamarin ya rikiɗe zuwa yaƙin basasa.

Burin samar da sauyi mai ma’ana tare da sake gina ƙasa cikin wani ƙayyadadden lokaci shi ne abin da ya biyo bayan wannan lamari wanda aka ɗorawa Manjo-Janar Aguiyi Ironsi alhakin jagoranta, amma abin takaici wannan mutum sai ya haifar da zargi tare da jefa kokwanto game da gaskiyar gwamnati a fannoni da dama. Wannan kuma ya gaurayu da abin baƙin cikin da ya auku ranar 15 ga watan Janairun 1966, wanda yake ɗanye shakaf a zukatan mafiya yawan jama’a, wani yankin ƙasa suka yanke shawarar bijirewa gwamnatin sojoja wacce kafin wannan lokacin ta ci moriyar samun gagarumin goyon baya.

Abin da ya biyo baya shi ne mummunan abin takaicin da ya haifar da zubar da jini wasu masu yawan daga cikin manyan birane da garuruwan Arewacin ƙasa. Lokacin da ya biyo baya mawuyacin hali ne wajen kwantar da hankulan jama’a har zuwa safiyar ranar 29 ga watan Juli na 1966, wanda a lokacin ƙasa ta sake faɗawa cikin wani mummunan yanayin kashe-kashe wanda ya zama karo na biyu a tsawon watannin bakwai. Lamarin da ya afku a safiyar ranar 29 ga watan Juli na 1966 shi ne kawo rahoto daga sansanin soja na Abeokuta cewa sojoji suna bore kuma har ta kai ga an kashe wasu manyan sojoji guda biyu haɗe da wani ƙaramin soja guda ɗaya daga wani yankin ƙasa. Cikin gaggawa abin ya yaɗu zuwa Ibadan da Ikeja. An kawo rahoton jikkata mutane da yawa daga guraren. Babban kwamanda a wannan lokacin yana Ibadan yana halartar taron sarakunan gargajiya wanda yake nufin komawa da yammacin ranar 29 ga watan Juli na shekarar 1966.

An kawo rahoton cewa an kai farmaki masaukin baƙin gwamnati wanda kuma rahoton ƙarshe da aka samu shi ne cewa shi da gwamnan soja na Yankin Yamma sojoji sun yi garkuwa da su. Har zuwa yanzun nan, ba a samu tabbaci game da takamaiman gurin da suke ba. Cikin ƙaramin lokaci aka sha kan matsalar a waɗannan guraren. Ba da jimawa ba kuma bayan an kammala wannan, sai aka samu irin waɗannan tashe-tashen hankulan a tsakanin rundunoni a arewa cewa wani tsagi na sojojin a Arewa sun karɓe ragamar jagorancin dukkan rundunonin da suke Arewa. Reshen da yake Enugu da kuma sansanin da yake Benin su abin bai shafe su ba. Yanzu komai ya daidaita, kuma zan iya bai wa jama’a tabbacin cewa zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen dakatar da duk wani zubar da jini a nan gaba tare kuma da dawo da doka da oda da kuma ƙarfin guiwa a dukkan sassan ƙasa tare da haɗin kai da kuma kyakkyawan fatanku.

Yanzu kuma na zo kan gaɓa mafi hatsari, a lokaci guda kuma mafi muhimmanci a cikin wannan jawabin nawa. Ina cike da damuwa matuƙa game da irin takaici tare kuma da ƙunan zuciyar da zai haifar a zukatan masoya Nijeriya na haƙiƙa da ma kuma haɗin kan ƙasa, a gida da kuma wajen ƙasa musamman ga ‘yan uwanmu na kwaman-welz.

‘Yan’uwana ‘yan ƙasa, ina da kyakkyawan fatan cewa za mu iya warware mafiya yawan matsalolin da suka rarraba kawunanmu a baya sannan kuma mu mutunta junanmu tare kuma da yarda da juna bisa dacewa da dukkanin sanannun kyawawan halaye da ɗabi’u.

Dukkan ‘yan ƙasashen waje, muna basu tabbacin tsaron lafiyarsu kuma cewa kada su ji tsoron cewa za a ci musu zarafi. Na ƙuduri aniyar ci gaba da aiki da manufofin da suke ƙunshe cikin jawabin babban kwamadan askawara na ranar 19 ga watan Janairu na shekarar 1966 wanda kuma aka wallafa shi a ranar 26 ga watan Janairun shekarar 1966. Kuma mu mutunta dukkan yarjeniyoyin ƙasa-da-ƙasa na wajibi da kuma saka hannu da kuma dukkan yarjeniyoyin kuɗi da aka ƙulla da gwamnatin da ta shuɗe. Muna da buƙatar ci gaba da kyakkyawar dangatar jakadanci da dukkan ƙasashen. Saboda haka muna la’akari da tsoma bakin wata ƙasa ta kowace fuska a matsayin bore. Kuma muna buƙatar dukkan mambobin rundunonin sojoji su ci gaba da zama a sansanoninsu, in banda waɗanda suke aiwatar da ayyuka na musamman ko kuma idan aka buƙace su daga Cibiyar Ƙoli. Tawagogin soja kada su musgunawa jama’a; kasantuwar yin haka zai zubar da mutuncin sabuwar gwamnatin sojan. Dukkan wani motsi na sata ko zagon ƙasa za a ɗauki matakin da ya dace.

Ku tuna cewa aikin ku shi ne taimakawa wajen dawo da doka da oda tare kuma da kwantar da hankalin jama’a a lokutan rigingimu. Na gamsu cewa da haɗin kanku tare kuma da fahimar juna, za mu iya tsamo ƙasar daga mawuyacin halin da take ciki yanzu.

Na yi muƙu alƙawarin cewa zan yi dukkan mai yiwuwa na mayar da ƙasar turbar dimokuraɗiyya da zarar an samu yanayin da za a iya shirya hakan. Kuma na ƙuduri aniyar hanzarta sakin fursunonin siyasa.

Yan’uwana ‘yan ƙasa, ku bani agajinku ni kuma zan ɗaukaka ƙasa kamar yadda ake saka rai.

Na gode muku, kuma sai da safe.

Ƙarshen Gwamnatin Janar Yakubu Gowon

A ranar 29 ga watan Juli na shekarar 1975, gwamnatin Janar Yakubu Gowon ta zo ƙarshe sakamakon juyin mulki da wasu sojojin suka yi a lokacin da shi Janar Gowon ɗin yake halatar wani taron haɗin kan ƙasashen Afirka (OAU) da ake gudanarwa a Kampala babban birnin Jamhuriyyar Uganda.

Wannan ce ta sanya ake gani a matsayin huce haushin da wasu sojoji suka yi biyowa bayan jawabin da Janar Gowon ɗin ya gabatar a ranar 1 ga watan Oktoban 1974 cewa maganar da ya yi ta miƙa mulki ga hannun farar hula a shekarar 1976 abu ne mai wahalar yiwuwa, saboda haka an ɗage wannan shiri har sai baba ta gani.

Gudun Hijirar Yakubu Gowon

Daga wannan rana ta 29 ga watan Julin shekarar 1975, kuma daga garin na Kampala babban birnin ƙasar Uganda, sai shugaban ƙasa Janar Yakubu Gowon ya ɗare jirgi zuwa ƙasar Ingila, ƙasar da ya zauna a cikinta har tsawon shekaru 8 (1975 – 1983), zaman da ya bashi damar shiga jami’ar Warwick tare da yin karatu a fannin kimiyyar siyasa a matakin digirin-digirgir wato Dakta abin rubta da PhD in Political Science a Turance.

Yanzu haka Janar Yakubu Gowon ya zama daya daga cikin dattawan Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan