Mun kashe sama da naira miliyan 400 a kan gangamin rigakafin cutar Polio – Ganduje

72

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kashe kudi fiye da Naira Miliyan Dari hudu da talatin kan gangamin yaki da cutar Polio a fadin jihar nan a wannan shekarar.

Kwamishina lafiya Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai kan shirye-shiryen fara yib allurar rigafin cutar a nan Kano.

Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce za’a fara gangamin rigakafin vutar polio daga gobe 31 ga watan Oktoba zuwa 3 ga watan Nuwamba, inda za a kaddamar da shirin a karamar hukumar Garko.

Kwamishin lafiyar ya kuma yabawa kokarin masu ruwa da tsaki a yakin da ake da cutar Polio tsawon shekaru goma wanda ya kai ga jihar ta kubuta daga cutar tsawon shekaru.

Idan za’a iya tunawa dai, a ranar 25 ga watan Agusta ne na shekarar 2020 a ka sanar da cewa yankin Afrika ya kubuta daga cutar bayan shafe shekaru hudu ba a samu dauke da cutar ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan