An gudanar da zanga-zangar ƙyamar Faransa a birnin Kano

187

Bayan kiran ƙauracewa kayayyakin Faransa, musulmi a birnin Kano sun gudanar da zanga-zanga domin ci gaba da nuna fushi kan kalaman shugaban ƙasar Faransa da kuma ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.

Tun da farko masu zanga-zangar sun fara tattaki da misalin ƙarfe 12 na ranar Lahadi daga Unguwar Gwammaja a ƙaramar hukumar Dala.

Masu zanga-zangar a birnin Kano na dauke da kwalaye da aka yi rubutun Allah wadai da shugaban ƙasar Faransa.

Mukhtar Nalele wanda shi ne shugaban masu zanga – zangar ya bayyana cewa, ya zama wajibi su nuna fushi a kan kalaman ɓatanci da shugaban Faransa ke yiwa addinin musulunci.

Haka kuma Mukhtar Nalele ya buƙaci al’ummar musulmi da su ƙaurace wa sayen kayan da aka yi shi a ƙasar Faransa domin yin tir da abin da ke faruwa.

Kazalika ya yi kira ga dukkan musulmai da su zama tsintsiya madaurinki daya.

Wannan zanga zangar dai na zuwa ne a lokacin da shugaba Emmanuel Macron ya sha alwashin kiyaye abin da aka san Faransa da shi a matsayin ƴar ba ruwana da kowanne addini.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan