Shirin Labarina Ya Samu Kyautar Yabo

101

Shararren shirin nan mai dogon zango, wato Labarina ya samu kyautar yabo a matsayin shiri mafi ƙayatarwa.

Mai bada umarnin shirin, Aminu Saira ne ya bayyana haka a shafunsa na Twitter da Facebook.

“Shirin #LABARINA Series ya samu lambar yabo. A madadin kamfanin Saira Movies da illahirin ma’aikatan wannan shiri na #LABARINA Series, muna miƙa godiya ga NIGHT OF FAME Award, 2nd Edition bisa ga wannan lambar yabo. Muna godiya ga masoya wannan shiri na duniya baki ɗaya”, in ji Mista Saira.

Shirin Labarina shiri ne mai dogon zango da yake nuna yadda ake badaƙalar soyayya tsakanin Mahmud (Nuhu Abdullahi) da Sumayya (Nafisa Abdullahi), kuma shirin yana ƙawatar da ɗimbin ma’abota kallon sa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan