Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afirka ta Yamma, WAEC, ta sanar da fitar da sakamakon Jarrabawar Kammala Babbar Sakandire ta Afirka ta Yamma, WASSCE, ta 2020.
Shugaban WAEC a Najeriya, Patrick Areghan ne ya sanar da haka ranar Litinin a shafin Twitter na WAEC.
Shugaban na WAEC a Najeriya ya ce jimillar ɗalibai 1,549,740 ne suka yi rijistar WASSCE ta 2020, yayin da ɗalibai 1,538,445 suka zauna jarrabawar.
A cewar Mista Areghan, daga cikin wannan adadi, ɗalibai 780,660 ne maza ne, 757,785 kuma mata, abin da yake wakiltar kaso 50.74 cikin ɗari da kuma kaso 49.26 cikin ɗari.
Turawa Abokai