Kukan Daɗi ASUU Ke Yi- Gwamnatin Tarayya

123

Yayin da Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, suke shirin ci gaba da tattaunawa a yau Laraba don samun mafita game da yajin aikin da ƙungiyar ke ci gaba da yi, Ƙaramin Ministan Ilimi Emeka Nwajiuba, ya ce “haƙiƙa babu abin da” ya hana malaman jami’o’in dawowa aiki ko da “gobe ne”.

ASUU da Gwamnatin Tarayya za su haɗu a yau a Babban Birnin Tarayya, Abuja, domin ci gaba da tattaunawarsu don warware matsalolin da suka sa ASUU ta tsunduma yajin aiki tun a Maris, 2020.

Mista Nwajiuba, wanda ya bayyana muhimmancin ci gaba da tattaunawa da malaman jami’o’in ya faɗa a wani shiri na gidan Talabijin na Channels mai suna “Politics Today” cewa, bisa yadda gwamnati take biyan buƙatun malaman jami’o’in, ba wani abu da ya kamata ya hana su dawowa aiki.

Ya ce: “Malaman jami’o’in za su iya komawa aji ko gobe ne idan suna son komawa.

“Ba abinda ya hana malaman komawa aji ko gobe ne.

“Gaskiya babu wani abu.

“Duk abinda ya kamata gwamnati ta yi ta riga ta yi.

“Idan kana son albashinka, ka hau tsarin ka karɓi albashinka”.

Da yake mayar da martani game zargin da ake yi cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta karɓi wani tsarin biyan albashi ba idan ba IPPIS ba, Mista Nwajiuba said: “Ni ban ce ba ce gwamnati ba za ta taɓa sauya matsayarta ba.

“Amma ina cewa ne wannan shi ne abin da muke da shi yanzu.

“Gwamnati za ta ci gaba da inganta aikinta.

“Idan yadda muke ci gaba da aiki UTAS ya zama tsarin da ya fi gamsar da kowa, kuma suka bada shi kyauta ga gwamnati, mu gwamnati ce mai jin kukan jama’a, cikin sauƙi za mu koma can”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan