Abin Takaici: Yadda Musulmai ke cirewa wasu sha’awar addinin a Arewa

146

Yanzu dai ta fito fili kowa ya fuskanci halayen wasu mutanen Arewa masu fakewa da sunan son addini su ci zarafin wasu saboda wani kuskure ko laifi da suka aikata a rayuwa. Abin takaicin ma shi ne abokan zamanmu har sun ganie wannan mummunan halin namu.

Musulunci addini ne da ya yadu ta sanadiyyar soyayya da tausayawa da jin kai da kuma yin uzuri wasu lokutan ma har da kawar da kai kan wasu laifuka ko kuskuren wadanda ake son su shiga addinin domin janyo su a jiki.

Sau da yawan gaske an sha samun wani yayi kuskure, sahabbai su yi ca amma Manzon rahma (SAW) ya taka musu birki. Misalin wani Bakauye da ya tsallara fitsari a cikin masallacin Annabi (SAW), lokacin da jama’a suka yi ca da nufin dakawa mai fitsarin tsawa, sai Manzon rahma (SAW) ya ce su kyale shi har sai ya kamala a tsanake.

Daga cikin dabarar yin hakan kuwa na farko dai mai yin fitsarin bakauye ne, na biyu babu kyau tsoratar da wani har ya firgita, na uku a fannin lafiya idan ya dakata ba tare da yin shiri ba fitsarin na iya yi masa illa, na hudu kuma ba shi da masaniyar akwai wata dokar da ta hana yin fitsari a wurin, sai kuma na biyar shi ne so ake a jawo shi a jiki.

… in takaice muku zance, bayan da ya waigo yaga ana ta yi masa muzurai sai yayi addu’a yace, Allah ya gafarta masa shi kadai da kuma Manzon Allah (SAW).

A tunaninku menene yasa yaki shigar da sahabban da suke wurin cikin addu’arsa?

Wata rana Manzon Allah (SAW) na zaune tare da jama’a sai ga wani mutum ya zo ya kira sunan shi kai tsaye, ya ce, tun da dukiyar baitul mali ba ta … (ya kama sunan iyayen Manzon Allah) ka shiga ka debo min rabo na!

Haka Abul Kassim ya tashi ya shiga ya debo masa kaya masu yawan gaske ya bashi.

A baya-bayan nan, a wani labari Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto yakan bayar da kyauta mai girma ga mutane, idan ya bawa wadanda ba Hausawa ba sai su rasa wurin sakawa; su kuma Hausawa sai su saka a babbar riga. Hakan ta sanya babu shiri ragowar kabilun suka koyi saka babbar riga.

To amma a yau wasu Musulmai bisa rashin fahimtar salo da dabarun da’awa (yada addini) sai su rika amfani da munanan kalamai masu kaushi da ciwo wasu lokutan har da zagi ga wadanda ba ma su musulunta ba ko kuma ga wadanda suka musuluntan.

Irin wadannan musulmai musamman a kafafen sadarwa na zamani kan sheke ayarsu tare da tata rashin mutunci da kuma goratawa wadanda suka musulunta ko kuma fadar bakaken maganganu kan wasu musulman da suka aikata laifi, kuskure ko zunubi.

Abin haushin ma shi ne sai ka ji suna magana kamar wadanda suke da tabbacin shiga aljanna, su rika kai mutum wuta suna nesanta shi da rahmar Allah. Sun manta da cewa shi kansa Manzon tsiran an aiko shi don ya kasance RAHMA ga talikai.

Hotunan Rahma Sadau da maganar Munirat Abdulsalam su ne saka sanya na dan yi wannan takaitacce rubutun.

Rahma Sadau

Duk da cewa dan kuka shi ke janyowa… Rahma Sadau ta nemi afuwa ta gane tayi kuskure saboda abinda hoton ya janyo, kuma ko baka sonta to dole dai zaka yarda bata yi wannan abin don ya kai ga inda ya kai ba, sai dai kuma wasu sun kai abin ma inda bai kamata ba.

Zaginta zai batar da abin ne daga faruwa? Ko kuma haka cin mutuncinta shi ne matakin da ya da ce bisa koyarwar musuluncin da kuke tutiya?

Adam Zango a shekarun baya har gorin Addini aka yi masa, abin haushin ma daga garin da suke tutiyar addini! Haka addinin ya koyar?

Adam A. Zango

Munirat Abdulsalam da ake ta yamadidi da ita yanzu dai ta fasa kwai, yanzu haka saki bidiyon da yake bayyana irin wahalar da ta sha da kuma wacce take kan sha kawai saboda ta zabi ta zama musulma. Amma aka rasa wadanda zasu bata tallafin da take bukata, goyon baya da ja a jiki tare da karfafa mata gwiwa.
Shin dama wai haka addinin yace ana yi?

Munirat Abdul-Salam

A ina masu yin irin wannan halin na kora da cirewa masu son shiga musulunci shawarsa suka samo wannan koyarwa?

Ashe dama duk sahabban da ake ji da su ba shiga musuluncin su ma suka yi ba ne? su ma ai sai ayi musu gorin!

“Sau da yawan gaske mutane zasu kasance masu aikata aiki irin na yan wuta daga karshe sai Allah (SWA) ya so su da rahma su rikide su karkare da aikata na yan Aljanna kuma su mutu akansa: Sau da yawan gaske mutane zasu yi ta aikata aiki irin na yan Aljanna amma kash daga karshe sai su rikide su koma aikata aiki irin na yan wuta kuma su mutu akan haka.” (Hadisi).

Shin kana da tabbacin shiga aljanna?
Ko kana da ikon sanya wani a wuta ko aljanna ne?
Kana da tabbacin ibadar ka ana karba ma kuwa idan da ita kake tutiya?

Wallahi sau da yawan gaske dabi’u da halayen wasu baragurbin musulmai ne ke hana yan uwanmu masu bin wasu addinin karbar addinin gaskiya na musulunci.

Mu yi wa’azi da salo da dabara da hikima da tausasawa.

Ina ma zamu gane mu fara tarairaya da kuma nuna kulawa ga masu aikata laifi ko kuskure ko kuma ga abokan zamanmu don su san cewa akwai abin kwarai na nunawa a addinin namu.

Duk da yake muslunci daban musulmai daban, amma wadanda ba musulmai ba basa gane haka yawancinsu.

Mu zama jakadu na gari ko ma kwatanta yadda magabata suka yi.

Abubakar SD
abubakarsd@live.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan