Sharhi: Talaka – Musulmi kuma Ɗan Arewa – Mukhtar Mudi Sipikin

  156

  Abubuwan da suke faruwa a Arewanci Najeriya suna da ban mamaki da ɗaure kai, sannan suna buƙatar amsoshin tambayoyi na gaskiya.

  Wai me ya sa Gwamnati Tarayya ke nuna halin ko in kulawa akan duk wata matsala da ta shafi Arewacin Ƙasar nan ne? Musamman ma matsalar da ta shafi Talaka, Musulmi kuma Ɗan Arewa?

  Sau da yawa in kun lura, za ku ga a ƙasar nan in har ka faɗo a wannan rukunin na Talaka, Musulmi sannan Ɗan Arewa, to ƙiri-ƙiri ake nuna maka ba ka isa komai ba, kai da banzar bazara ma da duk ɗaya ku ke, kai gwamma banzar bazarar ma da kai!

  Yanzu dai kalli yadda ake rashin imani a Katsina, Zamfara, Kaduna, Sakwato, Niger, Nassarawa da wasu jihohin na Arewa, amma da ya ke galibi wanda aka kashewa sun faɗa a wannan rukunin na Talakawa, Musulmai sannan Ƴan Arewa, za ku ga Gwamnati sam ba ta ba da kulawar da yakamata akai!

  Kai ko Jaridu sai da kawai ka ji suna faɗar “Figures” wato adadin wanda aka kashe ko aka sace, ka ji an ce an kashe mutum 20 an sace 50, ko an kashe 15 an sace 30! A haka dai kullum!

  Shi ke nan wai jama’a sun zama adadi kamar wasu tumaki! Ke nan ba su da wata daraja! A duk mutum ɗaya da aka kashe fa, yana da Uwa, Uba, Ƴan’uwa, Mata ko Miji da abokai wanda su ke jin raɗaɗin mutuwar kamar yadda mu ke ji in mun rasa makusantanmu! Amma dai tunda sun kasance Talakawa, Musulmai sannan Ƴan Arewa to su fa ba wata daraja ce da su ba, in kana son ka ga Gwamnati ta miƙe tsaye to a taɓa ɗan kudu ɗaya, Yanzu za ka ga hankalinta ya tashi!

  Ai mun ga yadda aka kashe wani Ɗan kudu ɗaya, da har sai da I.G na ƴan sanda ya ba da haƙuri, har mataimakin Shugaban Ƙasa shi ma sai da ya je ya ba da haƙuri! Su Ƴan kudu ba adadi ba ne, duk rai ɗaya mai daraja ne a Idon Gwamnati!

  Sau da yawa in abu ya shafi Talaka Musulmi kuma Ɗan Arewa, to sai yai ta ihu kamar ransa zai fita sannan Gwamnati ta ke ɗan waiwayarsa sannan ta ce ” za ta duba” Amma a kwana kaɗan Ƴan Kudu suka tilasta aka rushe SARS, aka tilastawa shugaban ƙasa jawabi, amma takwarorimsu #SecureNorth ko kallon su ba ai ba! Yo ina ruwan Gwamnati da Talaka Musulmi Ɗan Arewa!

  Yanzu ku duba yadda aka sace yara kwanaki aka kai su Kudu, aka canza musu sunayen sannan uwa-uba aka canza musu addini, amma da ya ke ƴaƴan Talakawa ne, Musulmai kuma Ƴan Arewa wani mataki aka ɗauka don daƙile abun nan gaba, wani zurfaffan bincike akai don gano sauran yaran da aka sace? Na karanta a wata jarida cewar an saki Matar da ke gaba-gaba wajen sace yaran!

  Yanzu da Ƴan Arewa ne kuma musulmi ya je ya sato yara daga kudu ya kawo su Arewa, da rai ya ɓaci. Ai dai mun ga izina akan Yunusa Yalo ai ko?

  Ku duba dai ku ga yadda ƙiri-ƙiri zanga-zangar #Endsars ta ƙare akan ƴan kasuwar Gwari a jihohin Kudu maso gabas, ai duk mun ga, kuma mun ji yadda aka kashe wasu sannan aka ƙona dukiyoyin musulmai, talakawa sannan Ƴan Arewa, amma sam ba ta su ake ba, ba maganar biyan diyya rayukansu ko biyansu ɓarna da akai musu ake yi ba.

  Amma sai ga shi Speaker Femi, har cewa ya ke lallai za su yi amfani da duk abun da su ke da shi wajen an gyara ɓarna da aka yi a Ikko, ɓarnar da su da hannunsu su ka yi, amma a ce a ɗauki kuɗin ƙasa a gyara. To banbamcin shi ne su na daban ne a idon Gwamnati, sannan waccen ƴan kasuwar tun da suna cikin rukunin Musulmai, Talakawa sannan Ƴan’ Arewa, to su da banza duk ɗaya su ke.

  Yanzu ai duk rashin imanin da ake na rashin tsaro a Arewacin Najeriya ka taɓa jin ƴan majalissun Arewa, Ko Senate da suka fito daga Arewa sun haɗu sun yi magana da murya ɗaya? Ko sun yi wa shugaban ƙasa barazanar tsigewa in har ba a ɗauki mataki ba, an shawo kan matsalar?

  Ko bayan meeting ɗin shan shayi da Gwamnoni Arewa ke yi in sun bushi iska akan harkar tsaro, ka taɓa ganin sun haɗu da su da sarakuna da duk wani mai faɗa a ji, akan kawo ƙarshen taɓarɓarewa al’amura a Arewa, kamar yadda Yarbawa su ka yi, har su ka samar da Ameotekum ta ƙarfi da ya ji?

  To dai duk amsar ɗaya ce, don matsalar ran Talaka, musulmi, Ɗan Arewa ta shafa, su kuwa wannan shugabannin duk da dai kafaɗar Talaka, Musulmi, Ɗan Arewa su ke takawa su ci zaɓe, to su fa Kare ko Magen gidansu, ya fi Talaka, musulmi Ɗan Arewa ƙima da a idonsu.
  Ƙimar talakawa, musulmai, Ƴan Arewa sai ko an zo zaɓe, ko kuma suna so su cimma wata manufar, ta ƙashin kan su.

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan