Tsarin karɓa-karɓa ba zai iya magance matsalolin Najeriya ba – El-Rufai

93

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa tsarin karba-karba ba shi ne zai iya magance tulin matsalar tattalin arzikin Najeriya ba.

Gwamnan ya yi wannan bayani a jawabin sa wurin Taron Makamar Tattalin Arziki na Kasa, inda ya ce karba-karba ba hanya ce ta tabbacin magance tattalin arziki ba.

Duk da tsarin karba-karba ba ya cikin tsarin mulki, amma jam’iyyu da ‘yan siyasar Najeriya na yin tsarin karba-karba tsakanin Arewaci da Kudancin Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari da ke kai a zango na biyu, ana sa ran bayan ya kammala, mulki zai koma a hannun kudancin kasar nan.

Cikin watannin nan batun maida mulki a hannun ‘yan kudu ya rika tayar da hayaki, har ta kai gwamnan jihar Ebonyi, David Omahi, ya fice daga PDP ya koma APC.

Umahi ya yi zargin cewa ya fice daga PDP, zuwa APC, saboda ya gano cewa PDP ba za ta bada takarar shugaban kasa a hannun dan yankin Kudu maso Gabas, wato yankin jihohin kabilar Igbo.

Shi ma Ministan Ayyukan Babatunde Fashola, wasu jaridu sun ruwaito shi ya na cewa a 2023 ya kamata mulki ya koma kudu.

Amma shi kuwa El-Rufai, cewa ya yi karba-karba ba zai fitar da Najeriya daga matsalar tattalin arziki ba. Don haka ya ce kamata ya yi a ba kowa ‘yanci da damar fitowa takara, sai a tantance a dauki guda daya kwakkwara mai nagarta.

Ko cikin watan Agusta sai da El-Rufai ya ce kamata ya yi a yi watsi da karba-karba, a bi cancanta kawai. Ya ce ko ma daga ina wanda ya fi cancanta ya ke, to sai a ba shi takara kawai.

Cikin Agusta kuma gwamnan na Kaduna ya ce bai kwamata ‘yan Arewa su tsaya takarar zaben shugaban kasa ba.

Cikin Oktoba 2019, tsohuwar babbar jami’ar diflomasiyya ‘yar Amurka, Linda Greenfield, ta ce siyasar Najeriya za ta samu kanta cikin yanayi mai tsauri idan zaben shugaban kasa na 2023 ya zo.

Ashafa Murnai

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan