Ko Me Yasa Mutum Ya Rataye Kansa A Kano?

144

Wani dattijo mai suna Ibrahim Abubakar, da aka fi sani da Iro, ya rataye kansa a shagonsa dake unguwar Zoo Road a cikin birnin Kano.

Iro, wanda yake siyar da batiran mota da tayoyi, an same shi ne a rataye lokacin da ‘yan sanda da maƙobtansa suka fasa shagon.

Shaidun gani da ido sun ce marigayi Iro ya halarci sallar La’asar tare da sauran jama’a, in da bayan nan kuma kowa ya koma shagonsa.

A kan hanyar koma wa shagonsa nasa ne sai marigayi Iro ya tsaya a shagon wani maƙobcinsa, in da ya karɓi igiya ya tafi da ita.

A lokacin da ya je shagonsa, sai ya aiki ɗansa da suke zama a shagon tare da nufin ya siyo masa abinci, ya kuma aiki wani mai shago shi ma kafin daga bisani ya kulle shagon ya kuma ya rataye kansa.

Lokacin da ɗan nasa ya dawo da abincin ya ga shagon a kulle, ya jira sosai, sai ya fara tunanin ko lafiya, ya kuma tambaya ko ina babansa yake.

Shi ma mai shagon da ya karɓi igiya a hannunsa sai ya fara zargin ko lafiya, sai ya sanar da ‘yan sanda, in da suka zo suka fasa shagon, suka samu gawar mutumin da igiya a rataye.

Har yanzu ‘yan sanda ba su ce uffan ba a kan wannan al’amari.

Har yanzu dai ba a gano dalilin da yasa marigayin ya rataye kansa ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan